Friday, July 26, 2019




Zangazangar 'Yan Shi'a ta dauki sabon salo

Home Zangazangar 'Yan Shi'a ta dauki sabon salo

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
A hakin da ake ciki dai zanga zangar da mabiya Shi'a ke yi a babban birnin tarayya Abuja domin a sako musu jagoran su Malam Ibrahim Zakzaky ta kai matuka a wannan mako da muke ciki a inda har ta kai ga rasa rayukan mutum 6 a ranar litinin da ta gabata,

'Yan sanda sun ce masu gudanar da wannan zangazanga sun kai akalla mutum 3000 mata da yara da samari kuma abun ya faro ne daga unguwar Wuse sai suka nufi sakatariyar tarayya karfe 12 na ranar litinin din a inda hakan ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi,

A wata sanarwa da ta fito daga hannun mai magana da yawun 'Yan sanda na kasa DSP Frank Mba ya ce masu wannan zangazanga sun kai hari ga 'Yan sanda ne dake kusa da sakatariyar tarayya wanda a yunkurin su na hana su isa wajen ne DSP Usman Umar ya rasa ran sa.

Bayan haka 'Yan sanda sun sanar da rasuwar wani Dan jarida mai suna Precious Owolabi a yayin artabun jami'an tsaro da mabiya Shi'a sannan wadansu jami'an yan sanda masu mukamin ASP sun dan samu raunuka,

Sai dai suma masu zanga-zangar daga nasu bangaren sun ce kimanin mutane 30 ne suka jikkata"

Rundunar 'Yan sanda ta ce nan ba da dadewa ba zata gurfanar da wadanda ta kama a ganban kutu bayan ta gama bincike a kan su.


A ranar Talatar da ta gabata ma ’yan kungiyar IMN sun sake gudanar da wata zanga-zangar a Unguwar Wuse 2 a Abuja. Sai dai tun a farkon taruwarsu ’yan sanda suka tarwatsa su, suka kama wadansu.

’Yan Shi’ar sun yi jana’izar mutum 6 a Suleja da ke Jihar Neja a yammacin ranar, wadanda suka ce ’yan sanda ne suka kashe a zanga-zangar ranar Litinin.


Masu shawartarmu da cewa mu jingine zanga-zangar mu rungumi tuntubar manya don neman a saki Sheikh Elzakzay ba su yi mana adalci ba. A cewar wani mai magana da yawun mabiya Shi'a “Babban dalilin da ya sa muke wannan muzahara da kara tsananta ta a yanzu shi ne, sakamakon bincike da wasu likitoci da suka zo daga waje ya nuna cewa yana dauke da guba. To gubar nan kuma ta kisan mummuke ce. Wannan ya sa muka zafafa kira na lallai sai a sake shi kamar yadda kotu tun farko ta ba da umarni, ko akalla a ba shi dama ya je a duba lafiyarsa. Kuma su mahukuntan idan ba sa son wani abu sai su kirkiri wata karya don su samu damar aukawa a kanmu, su ce mun yi wani abu.”

Game da zargin cewa ’yan kungiyar na da hannu a kashe Mataimakin Kwamshinan ’Yan sandan Abuja, Malam Abdulhamid Bello ya ce “Lamarin a fili yake saboda yanzu ana daukar komai a waya da sauransu. Sai su nuna lokacin da ya iso wajen da lokacin da yake magana da ’yan uwa tare da gudanar da cikakken bincike a lamarin. Amma duk ba su yi haka ba, sai kawai suka yi sauri suka binne shi ba tare da yin wadannan abubuwan ba. Ba za mu taba yarda da wannan zargin ba, don ba aikinmu ba ne kuma ba mu taba yi ba kuma idan ma harbin nasa ne aka yi, to wani daga cikinsu ne ya aikata kamar yadda suka saba yi. Su kashe dan uwansu, su ce wani ne ya kashe shi.”

Ya ce, sun tabbatar da kashe musu mutum shida, kuma suna da yakinin akwai wasu gawarwakin jama’arsu da ba a mika musu ba.

A baya-bayan nan dai zangar-zangar ta ’yan Shi’a da ta dauki sabon salo, ta rutsawa da jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, musamman ma ma’aikatan gwamnati kko masu kai ziyara a wasu ma’aikatu, inda a wani zubin ake lalata motoci ta hanyar fasa gilasansu sakamakon jifa ko rubuce-rubuce da jan fenti a jikinsu da ake rubuta “A Saki Zakzaky.” Rubuce-rubucen sun hada har da a jikin gine-genen ma’aikatu da kuma gefen titi.

Ko a ranar Litinin, an banka wuta ga wata karamar cibiyar Hukumar Agajin Gaugawa (NEMA) da ke  kusa da Sakatariyar Tarayya kuma kusa da wasu muhimman wurare, kamar Ma’aikatar Kudi da ta Harkokin Kasar Waje da Majalisar Dokoki da Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli da  kuma daya daga cikin mashigar Fadar Shugaban Kasa.

A jawabin da ya yi bayan ziyarar gani da ido, Babban Daraktan Hukumar NEMA, Injiniya Mustafa Maihaja ya zargi ’yan Shi’ar da kona musu motoci biyu da suka hada da ta tafi-da-gidanka don daukar marasa lafiya da motar daukar gawarwaki.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.