Showing posts with label ZAUREN LABARAI. Show all posts
Showing posts with label ZAUREN LABARAI. Show all posts

Wednesday, October 30, 2019

[[Karanta]] A gaskiya ni ban iya Hausa ba Zahra Buhari

[[Karanta]] A gaskiya ni ban iya Hausa ba Zahra Buhari

'Yar Shugaban kasa Zahra Buhari ta bayyana cewa ita fa bata iya magana da harshen Hausa sosai ba.

Zahra Muhammadu Buhari ta bayyana hakan ne a yayin wani taro da gidan Radion BBC ya shirya domin wadanda suka lashe gasar gasar da suke gabatar wa mai tajen 'HIKAYATA' wanda suka saba shirya wa ko wace shekara a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja,
Mahaifin Zahra wato Shugaba Muhammad Buhari dai kamar yadda kowa ya sani Bafullatani ne garin Daura na jihar Katsina haka ma mahaifiyar ta matar shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ita ma Bafullatana ce daga jihar Adamawa,

Zan baku mamaki domin bazan iya magana da hausa ba domin ko a gida idan ina magana da Hausa baban mu dariya yake yi mun inji Zahra"


Ta cigaba da cewa “Munyi rayuwar makaranta ne da fararen fata sannan kuma muna hada Hausa da turanci ne idan muna magana a gida” A karshe ta bayyana cewa yawanci a gida suna magana ne da fulatanci Wanda hakan yasa Hausa take yi mata wahala.

Monday, October 14, 2019

Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

A kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka cika da jita jitar cewar Shugaba Muhammadu Buhari zai kara aure da kuma cewar uwar gidan sa wato A'isha Buhari ta yi yaji.

Source: voahausa.com


Hajiya Aisha Buhari, da ta kwashe kusan watanni biyu ba a ji duriyarta ba a Najeriya ta koma gida yau Lahadi daga kasar Birtaniyya. A lokacin da ta isa tashar jiragen saman birnin tarayya Abuja ‘yan jarida sun yi ma ta ca da tambayoyi akan abin da ke faruwa.
Hajiya Aisha ta bayyana cewa ta je ganin ‘yayanta ne a Birtaniyya, abinda kamar wata al’ada ce a garesu ta zuwa hutu a lokacin da suka sami dama. Ta kuma ce ta sami damar a duba lafiyar ta a London saboda ba ta ji dadin jikinta ba.
Da take maida martani game da jita jitar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai auri Ministar ayyukan jinkan Najeriya Hajiya Sadiya Umar Farouq, Hajiya Aisha ta ce ba ta da masaniya akan abinda ya faru tun da ba ta nan, amma wanda aka ce zai yi auren ne ya kamata ya yi bayani.
“Amma ita wadda aka ce za a aura, wanda ya gaya mata za a aure ta, ba ta yi zaton ba a daura auren ba, don sai da ta ji shiru ba labari sannan ta fito ta musanta batun,” a cewar Hajiya Aisha.
Game da batun yajin da aka ce ta yi, uwar gidan shugaban ta ce tun da aka ce mai gidanta (Shugaba Muhammadu Buhari) ya mutu lokacin da ya je London jinya to ba jita jitar da jama’a ba zasu iya yadawa ba.

Tuesday, September 17, 2019

Yabon Mahtama Ghandi Ga Annabi Muhammad S.A.W

Yabon Mahtama Ghandi Ga Annabi Muhammad S.A.W

An gayyaci Mahatma Ghandi wani taro ranar 23 ga watan june 1934 a Islamabad kasar Pakistan cikin jawabin sa lokacin da ya zo yin magana game da Annabi Muhammad S.A.W ga abun da yace,

A lokacin da aka tsare ni a kurkuku a India na samu damar Karanta wani littafi na Maulana Shibli akan Rayuwar Muhammad S A W. Kuma na fahimci cewa Muhammad Mutum ne mai Gaskiya,Mai Tsoron Ubangiji"

Nasan cewa ba wani abu sabo nake gaya muku ba amma inaso na bayyana muku yadda Rayuwar sa tayi matukar birgeni."

Ya Hadu da cutarwa mai yawa, shi mai matukar Jarumta ne kuma baya tsoron kowa face Ubangiji shi kadai. Ba'a taba samun sa da fadar wata magana ba tare da ya cika wannan maganar ba. inya so ma zai iya rokon ubangiji ya mai dashi mafi Kudin duniya amma baiyi hakan ba."

Ba iya mahatma Ghandi ba akwai mutane sanannu masu dimbin yawa da suka yabi Annabi Muhammad S A W.

Friday, August 30, 2019

WASIKAR MALAM IBRAHIM SHEKARAU GA GWAMNAN RIBAS

WASIKAR MALAM IBRAHIM SHEKARAU GA GWAMNAN RIBAS

Tsohon gwamnan jihar kano kuma sanatan kano ta tsakiya a yanzu mai girma Malam Ibrahim Shekarau ya aike da Damon mayar da martani ga gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike dangane da rushe Masallacin Juma'a da aka yi a jihar sa,

Dardaunan na Kano yayi kira da babbar murya ga yan Nigeria da suyi Allah wadai da abun da gwamnan Ribas na rushe wurin ibadar Musulmai dake a unguwar Trans Amadi babban birnin Fatakwal
A inda ya ci gaba da cewa munji gwamnan Ribas yayi alwashin ba zai bada hakuri game da abun da ya aiwatar ba wanda hakan rashin adalci ne da kuma ganganci da ma yunkurin tayar da husuma cikin kasa, "

Yanzu idan aka samu wani gwamna Musulmi ya ayyana jihar sa a matsayin jihar Musulmai zalla sannan ya rika bi yana rushe coci coci zaka ji duniya ta yi ca akan hakan kuma mabiya Addinin kirista zasu nemi agajin kungiyoyi na kasashen duniya har ma da majalisar dinkin duniya,

Haka ma da wani gwamna Musulmi zai furta munanan kalamai game da kirista kwatankwacin na gwamna Wike to da hakan zai girgiza Nigeria ta yadda zai jawo mabiya Addinin kirista su yi ca a kan sa sai dai abun takaici munga wasu shuwagabannin kirista na wannan kasa suna goyon bayan abun da gwamnan Rivas ya aikata inji Malam Shekarau

Yaci gaba da cewa Nigeria kasarmu ce gaba daya babu wata jiha da ke da ikon ayyana wani Addini kwaya daya a matsayin Addinin ta sanin darajar shugabanci shi ne ka rungumi kowa naka ne,

Idan za'a iya tuna wa lokacin da na zama gwamnan jihar Kano daga Shekarau 2003 zuwa 2011 mun karfafa mutane da su gudanar da rayuwar su a bisa tsarin shari'ar Musulunci amma hakan bai sa mun yi amfani da wannan dama wajen rushe wajen ibadar kiristoci ba,"
sannan ba mu yi amfani da damar da tsarin Mulkin kasa na kwansitushin sashi na 10 da ya bamu ikon ayyana jihar Kano a matsayin jihar Musulunci ba..

Abinda muka yiwa jama'ar Kano na adalci hakan ya jawo an yabe mu, mun samu yabo hatta daga kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) reshen jihar Kano a lokuta da dama, wadannan shugabannin kiristoci da suka yabemu har yanzu suna raye, zasu iya tabbatar da abinda nake fadi, ya kamata gwamnan jihar Rivers ya san da cewa; Mr Tala Ilo daga jihar Bayelsa da Mr. Chris Chibuzor Azuka daga jihar Anambra dukkansu mabiya addinin kirista ne, amma sun kasance daga cikin masu bani shawara na musamman lokacin da nake gwamnan jihar Kano...


Nyesom Wike yayi alwashin cewa Rivers jihar kiristoci ne zalla, wannan zancen banza ne da rashin hankali, ba dukkan mutanen dake Rivers ne mabiya addinin kirista ba, ba daidai bane jihar Rivera ta zama na kiristoci zalla kamar yadda ba daidai bane ace musulmai da sauran mabiya addini da suka fito daga sassan Nigeria su dauki jihar Rivers a matsayin jihar su su kadai ba, sannan Nyesom Wike yana gudanar da jihar Rivers bisa tsari na dokoki wanda ba irin na gwamnatin Nigeria ba, wannan ya nuna mana gwamnatin Rivers bata dauki wasu daga cikin manyan jiga jiganta musulmai 'yan asalin jihar ba a matsayin 'yan jihar Rivers, saboda kasancewarsu musulmai, irinsu Alabo Mujahid Dokubo Asari, Alhaji Isa Boaima, Alhaji Sani Okiri, Alhaji Ahmed Sani Pe, Alhaji Abdul’aziz Pepple, Alhaji Sulaiman Akani, Alhaji Ibrahim Orlu, Alhaji Musa Brown, Chief Hassan Douglas da Alhaji Mustapha Wakama
Sardaunan Kano yaci gaba da cewa; Ba wannan bane karo na farko da gwamnan Rivers Nyesom Wike yake bayyana wautarsa da rashin hankali ba, idan za'a tuna shekaran da ta gabata, yayi barazanan cewa zai rushe shugabancin jam'iyyarsa ta PDP idan har sukaki gudanar da babban taron jam'iyyar a birnin Fatajwal jihar Ribas, abin mamaki kuma sai suka biye wa wannan marar mutunci suka je suka gudanar da taron a inda ya bukata

Matakin da gwamnan Rivers yake dauka da irin munanan kalmomin da yake furtawa yana bayyana irin mutanen da basu cancanta ace sune jagororin al'umma ba, abinda yakeyi kokari ne wajen wargaza tsarin mulkin demokaradiyya a wannan kasa, sannan babban barazana ne da kalubale wa zaman lafiyar kasa, don haka muna kira ga gwamnatin Nigeria da dukkan hukumomin tsaron Nigeria da su fadakar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, sannan a tabbatar mishi da cewa idan ya kuskura ya kunna wutar rikici a Kasar zai girbi sakamakon abinda ya aikata
Daga karshe, ina kira ga musulmai mazauna jihar Rivers da dukkan Musulmai a Nigeria gaba daya da su kwantar da hankali, sannan su kasance masu da'a da bin doka, kar mu kwaikwayi mummunan dabi'a na Nyesom Wike, a cikin 'yan uwansa kiristoci akwai mutanen kirki masu son zaman lafiya, kar mu bari hankali da tunaninmu ya gushe mu je mu aikata ba daidai ba, kamata yayi mu karfafi 'yan uwanmu musulmai na jihar Rivers da su tsaya akan imaninsu, su mayar da hankali wajen bin matakin doka a kotu su kwato hakkinsu kamar yadda suka taba yin haka a baya, wannan karon zasu bukaci a sake gina musu Masallacin da aka rushe a Trans-Amadi, sannan a biya diyyah, bayan haka su bukaci gwamna Nyesom Wike ya fito ya bada hakuri wa 'yan Nigeria.

Friday, August 2, 2019

Ana siyasantar da batun Alzakzaky Sheikh Bala Lau

Ana siyasantar da batun Alzakzaky Sheikh Bala Lau

A dai dai lokacin da yake gabatar da hudubar Juma'a shugaban kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'a Wa Iqamatus Sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau Yayi Kira ga gwamnatin Nigeria ta yiwa Sheikh  Alzakzaky adalci.
Shehin malamin Addinin yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar da hudubar Juma'a a Masallacin JIBWIS da ke unguwar Utaku a Abuja
Ba wannan ne karo na farko da Malam Bala Lau ke magana game da batun Malam Zakzaky ba,
Idan ba a manta ba a baya ma Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa ya duba batun Malam Zakzaky kuma yana da kyau ya sallameshi" Sheikh Bala Lau yaci gaba da cewa ko kafiri ne yayi ba dai dai ba a hukunta shi amma ayi masa adakci,


Ya ci gaba da cewa: "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi abin da suka ga dama domin a saki shugabansu.
"Daga nan babu sauran zaman lafiya kenan," in ji shi.

Ya ce: idan idan an tabbatar jagoran mabiya Shi'a din bai aikata laifi ba to kawai a sake shi idan kuma laifi ya aikata to ayi masa hukunci na adakci kamar ko wane cikakken dan kasa haka ne zai kawo wa kasa zaman lafiya mai dore wa."
Hakika bana jin dadin yadda wadansu mutane ke siyasantar da batun nan" domin akwai masu kokarin amfani da wannan batu domin hada fitina a wannan kasa ta hanyar cewa idan aka gama da yan Shi'a za'a dawo kan yan darika ne kuma wannan ba dai dai ba ne magana ce da zata iya haifar da tashin hankali wanda muna fatan Allah ya tsare,"
Ya kara da cewa 'yan darika sun fi kusa da 'yan Izala fiye da kusancin su da 'yan shi'a.
Da ya dawo batun rahoton BBC dangane da Muhammad Yusuf Shehin Malamin Bala Lau cewa yayi hakika #BBC tayi kuskure da ta danganta tsohon shugaban kungiyar Boko Haram din da cewa yayi karatu a Jami'ar Musulunci dake Madina,
Labarin an wallafa shi ne saboda cika shekara 10 da aka yi da fara rikicin Boko Haram a Najeriya.
Sheikh Bala Lau ya yi kira ga BBC din da ta gaggauta gyara kuskuren da ta yi.
Sai dai tuni BBC ta gyara wannan kuskure 'yan sa'o'i bayan wallafa labarin kuma ta nemi gafar.

Monday, July 29, 2019

Yadda ake samun kudi a Instagram

Yadda ake samun kudi a Instagram

Ko kun san da cewa kafar sadarwa ta Instagram wannan da kuka sani kuma kuke amfani da ita kusan kullum akwai mutane da ke samun magudan kudade da ita kuma cikin sauki ba tare da wani wahala ba?

Ku biyo ni kusha labari.


Ga kadan saga cikin mutanen da suka fi samun kudi ta hanyar wallafa sako a Instagram,

1: Kylie Jenner yana samun zunzurutun kudi har Dala miliyon 1.2 a duk lokacin da ta wallafa wani sako a Instagram,

Hakan ne yasa ta zamo ta farko wajen samun kudi a Instagram cikin wannan shekara ta 2019,
Ko a shekarar da ta gabata ma Kyelie wacce ke da mabiya miliyan 141 a Instagram ita ce sahun farko wajen samun kudi a Instagram



Tsarin da ake bi wajen yin hakan sun hada da duba yawan mabiyan da fitattun mutane ke da su, da kuma yawan yadda aka sake aika abin da suka wallafa ko kuma tsokacin da aka yi a kai.


2: Shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo yana samun kudi dala 975000 a duk sako da ya wallafa a Instagram din,
Duk da cewa shine ya fi kowa yawan mabiya a Instagram a inda mabiyan sa sun kai miliyan 177.

3: Ariana Grande Tana samun dalar 966000 a duk sakon data rubuta a Instagram,

Mutanen da suka zama na gaba-gaba wajen samun kudi a Instagram cikin masu yawan mabiya sun hada da:


Selena Gomez da Dwayne 'The Rock' Johnson da Beyoncé da Taylor Swift da Neymarda kuma Justin Bieber su ne sauran wadanda suka biyo bayan wadancan cikin mutum 10.

Ana yawan sukar al'adar biyan fitattun mutane makudan kudade don wallafa wa miliyoyin mabiyansu sako.

Wasu na cewa mabiya na iya sauya dabi'unsu ko ra'ayinsu kan wani abu da aka wallafa, idan sun san cewa wadanda suke bi "sau da kafa" din za su samu kudi kan sakon da suka wallafa.

Masu suka sun kuma ce hakan na sa wa matasa su kasa gane hakikanin abin da suke so ko son cimma a rayuwa idan suka ga irin kudin da fitattun mutane ke samu daga wallafa abu.

Amma wasu na ganin hakan ba wata matsala ba ce a masana'antar fitattun mutane da tuni sana'arsu ke kawo musu miliyoyin fama-famai.


Friday, July 26, 2019

Zangazangar 'Yan Shi'a ta dauki sabon salo

Zangazangar 'Yan Shi'a ta dauki sabon salo

A hakin da ake ciki dai zanga zangar da mabiya Shi'a ke yi a babban birnin tarayya Abuja domin a sako musu jagoran su Malam Ibrahim Zakzaky ta kai matuka a wannan mako da muke ciki a inda har ta kai ga rasa rayukan mutum 6 a ranar litinin da ta gabata,

'Yan sanda sun ce masu gudanar da wannan zangazanga sun kai akalla mutum 3000 mata da yara da samari kuma abun ya faro ne daga unguwar Wuse sai suka nufi sakatariyar tarayya karfe 12 na ranar litinin din a inda hakan ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi,

A wata sanarwa da ta fito daga hannun mai magana da yawun 'Yan sanda na kasa DSP Frank Mba ya ce masu wannan zangazanga sun kai hari ga 'Yan sanda ne dake kusa da sakatariyar tarayya wanda a yunkurin su na hana su isa wajen ne DSP Usman Umar ya rasa ran sa.

Bayan haka 'Yan sanda sun sanar da rasuwar wani Dan jarida mai suna Precious Owolabi a yayin artabun jami'an tsaro da mabiya Shi'a sannan wadansu jami'an yan sanda masu mukamin ASP sun dan samu raunuka,

Sai dai suma masu zanga-zangar daga nasu bangaren sun ce kimanin mutane 30 ne suka jikkata"

Rundunar 'Yan sanda ta ce nan ba da dadewa ba zata gurfanar da wadanda ta kama a ganban kutu bayan ta gama bincike a kan su.


A ranar Talatar da ta gabata ma ’yan kungiyar IMN sun sake gudanar da wata zanga-zangar a Unguwar Wuse 2 a Abuja. Sai dai tun a farkon taruwarsu ’yan sanda suka tarwatsa su, suka kama wadansu.

’Yan Shi’ar sun yi jana’izar mutum 6 a Suleja da ke Jihar Neja a yammacin ranar, wadanda suka ce ’yan sanda ne suka kashe a zanga-zangar ranar Litinin.


Masu shawartarmu da cewa mu jingine zanga-zangar mu rungumi tuntubar manya don neman a saki Sheikh Elzakzay ba su yi mana adalci ba. A cewar wani mai magana da yawun mabiya Shi'a “Babban dalilin da ya sa muke wannan muzahara da kara tsananta ta a yanzu shi ne, sakamakon bincike da wasu likitoci da suka zo daga waje ya nuna cewa yana dauke da guba. To gubar nan kuma ta kisan mummuke ce. Wannan ya sa muka zafafa kira na lallai sai a sake shi kamar yadda kotu tun farko ta ba da umarni, ko akalla a ba shi dama ya je a duba lafiyarsa. Kuma su mahukuntan idan ba sa son wani abu sai su kirkiri wata karya don su samu damar aukawa a kanmu, su ce mun yi wani abu.”

Game da zargin cewa ’yan kungiyar na da hannu a kashe Mataimakin Kwamshinan ’Yan sandan Abuja, Malam Abdulhamid Bello ya ce “Lamarin a fili yake saboda yanzu ana daukar komai a waya da sauransu. Sai su nuna lokacin da ya iso wajen da lokacin da yake magana da ’yan uwa tare da gudanar da cikakken bincike a lamarin. Amma duk ba su yi haka ba, sai kawai suka yi sauri suka binne shi ba tare da yin wadannan abubuwan ba. Ba za mu taba yarda da wannan zargin ba, don ba aikinmu ba ne kuma ba mu taba yi ba kuma idan ma harbin nasa ne aka yi, to wani daga cikinsu ne ya aikata kamar yadda suka saba yi. Su kashe dan uwansu, su ce wani ne ya kashe shi.”

Ya ce, sun tabbatar da kashe musu mutum shida, kuma suna da yakinin akwai wasu gawarwakin jama’arsu da ba a mika musu ba.

A baya-bayan nan dai zangar-zangar ta ’yan Shi’a da ta dauki sabon salo, ta rutsawa da jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, musamman ma ma’aikatan gwamnati kko masu kai ziyara a wasu ma’aikatu, inda a wani zubin ake lalata motoci ta hanyar fasa gilasansu sakamakon jifa ko rubuce-rubuce da jan fenti a jikinsu da ake rubuta “A Saki Zakzaky.” Rubuce-rubucen sun hada har da a jikin gine-genen ma’aikatu da kuma gefen titi.

Ko a ranar Litinin, an banka wuta ga wata karamar cibiyar Hukumar Agajin Gaugawa (NEMA) da ke  kusa da Sakatariyar Tarayya kuma kusa da wasu muhimman wurare, kamar Ma’aikatar Kudi da ta Harkokin Kasar Waje da Majalisar Dokoki da Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli da  kuma daya daga cikin mashigar Fadar Shugaban Kasa.

A jawabin da ya yi bayan ziyarar gani da ido, Babban Daraktan Hukumar NEMA, Injiniya Mustafa Maihaja ya zargi ’yan Shi’ar da kona musu motoci biyu da suka hada da ta tafi-da-gidanka don daukar marasa lafiya da motar daukar gawarwaki.