Showing posts with label ZAUREN BOLLYWOOD. Show all posts
Showing posts with label ZAUREN BOLLYWOOD. Show all posts

Monday, October 28, 2019

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Jarumi Akshay Kumar yana daya daga cikin taurari a masana'antar Bollywood a yau zamu kawo muku wadansu cikin Faina-finan sa tare da shekaraun fitar su.

Ku biyo ni.

1: Saugandh, Ya fita a shekarar (1991)

2: Khiladi, Ya fita a shekarar (1992)

3: Waqt hamara hai, Ya fita a shekarar (1993)

4: Sainik, Ya fita a shekarar (1993)

5: Yeah dillagi, Ya fita a shekarar (1994)

6: . Main Khiladi Tu Anari. Ya fita a shekarar (1994)

7:  Mohra, Ya fita a shekarar (1994)

8: Sabse Bada Khiladi, Ya fita a shekarar (1995)

9:  Khiladiyon Ka Khiladi, Ya fita a shekarar (1996)

10: Dil To Pagal Hai, Ya fita a shekarar (1997)

11: Mr. & Mrs. Khiladi, Ya fita a shekarar (1997)

12: Sangharsh, Ya fita a shekarar (1999)

13: Jaanwar, Ya fita a shekarar (1999)


14: Hera Pheri, Ya fita a shekarar (2000)

Akshay Kumar yana da daruruwan shahararrun fina finai amma duk da haka zamu dakata a nan sai kun sake jin mu a karo na gaba.

Saturday, October 26, 2019

Friday, October 25, 2019

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

A rana mai kamar ta yau ne 25 ga Satan October auren fitattun jaruman nan na masana'antar Bollywood wato Sharukh Khan da matar sa Gauri Khan ya cika shekaru 28 cif,


An daura auren ne 25 ga watan October shekarar 1991,


Har yanzu dai masoyan biyu suna zaman su cikin koshin lafiya a matsayin ma'aurata a inda Allah ya arzuta su da 'ya'ya 3 a tsawon wadannan shekaru.

'Ya'yan nasu su ne Aryan Khan,
Suhana Khan, AbRam Khan,

A wannan karo ma masoyan sun shirya kayataccen biki tare da gayyatar 'yan uwa da abokan arziki da masoya,

Ma'auratan 2 Sharukh Khan wanda mabiyin Addinin Musulunci ne da matar sa Gauri Khan wacce ke bin Addinin Buddha sunan so ba zai taba mantuwa ba a Bollywood.

Sunday, September 29, 2019

[Bollywood]  Me kuka sani game da Amrish Puri

[Bollywood] Me kuka sani game da Amrish Puri

Me kuka sani game da Amrish Puri [Mugyambo,]


Kusan dai kamar yadda kowa ya sani jarumi "AMRISH PURI" babbar inkiyar sa wacce yayi Suhura da ita ta fannin suna a duniyar fim a nan kasar hausa itace : "MUGYAMBO",
Ga dukkan wadanda suka kasance suna bibiyar fina-finan sa sun san cewa Jarumi AMRISH PURI ko kuma ince MUGYAMBO yayi matukar kaiwa kololowa wajen iya shirya TUGGU da MAKIDA da DASISA, haka zalika ya goge sosai wajen iya shirya HIYANA da dukkan wata kitimurmura,


Baya ga haka kuma shi din shaharren mugu ne kuma azzalumi ajin farko, amma fa duk acikin duniyar fim (ba wai a duniyar azahiriyya ba),
A fagen iya acting kuwa da isar da sako yadda mai kallo zai gamsu ainun-ainun, to fah magana ta gaskiya ni dai kam a wuri na sam-sam har wa yau bashi da madadi,
Domin kuwa kusan dukkanin kafatanin rubunan fina-finan sa babu na yarwa, matukar ka ganshi acikin fim to ka kalla kawai, domin baya hawa fim marar ma'ana,

Na kalli tarin tulin fina-finan sa masu yawan gaske, fim dinsa na farko da na fara kalla shi ne fim din "GHAYAL", na kalli fim din shekaru kusan 21 da suka shu'de ranar lahadi da misalin karfe 11:15
Daga nan kuma sai irinsu

- GATAK,
- SALAAKHEN,
- JEET,
- KOYLA,
- LOHA,
- DAMINI,
- DILWALE DIL HANIYALE JAYENGE
- BADAL, etc,

Nasan cewa wanda duk ya kalli wadannan fina-finan dana lissafo lallai zai amintu da batutuwan da na zayyano game da wannan  Jarumin mai suna "AMRISH PURI" wato MUGYAMBO,
Malam MUGYAMBO akwai kurari da muzurai da nuna isa da tumbatsa, da kuma barazana, amma fa idan akwai basawan a kusa dashi, idan kuwa basawa suka kare to fah baya kasala wajen arar kafar Kare matsera.


Tuesday, September 17, 2019

Jarumai mabiya adinnin Hindu da suka auri mata Musulmai a Bollywood

Jarumai mabiya adinnin Hindu da suka auri mata Musulmai a Bollywood

A yau muna dauke da sunayen wadansu shahararrun jaruman Bollywood wadanda ba Musulmai ba amma sun auri mata Musulmai,

Ga sunayen ma'auratan kamar haka..,

1: Sanjay Duty ya auri Manyata Dutt a ranar 7 ga watan February na shekarar 2008 asalin sunan ta shi ne Sarah Khan Musulma ce ta haifa masa 'yan biyu mace da namiji,

2: Hrithik Roshan ya auri Sussanne Khan ranar 20 ga watan December shekarar 2000 sun rabu a 2014 sun haifi 'ya'ya biyu,

3: Sunil Shetty ya auri Mana Qadri a shekarar 1991 Allah ya azurta su da 'ya'ya biyu,

4: Aditya Pancholi ya auri Zarina Wahab a shekarar 1986 suma sun haifi 'ya'ya biyu ne,

5: Atul Agnihotri ya auri Alvira Khan cikin shekarar 1996,

A takaice wadannan su ne jerin jarumai maza wadanda ba musulmai ba amma sun auri mata Musulmai a Bollywood.

Muna fatan Allah ya tsare mana imanin mu.


Monday, July 22, 2019

Manyan jaruman Bollywood kuma mawaka

Manyan jaruman Bollywood kuma mawaka

A yau zamu kawo muku jerin sunayen wadansu jaruman fim na kasar India da suka taba rera wakar Fim da kan su,

Ba tare da bata lokaci ba ga jerangiyar jaruman #Bollywood da suka rera wakoki da kan su

1. Amitabh Bachchan,
Wannan sanannan tsohon jarumin mazan jiya ya rera waka da kan sa cikin Fina-finai kamar haka. Silsila, Toofan, Baghbaan, Baabul, da dai sauran su wato bama sau daya ne ya rera waka ba,

2. Amir Khan.
Wannan jarumi mai suna a sama shima ya rera wakoki da dama cikin Finafinai kamar Ghulam, Dangal, Taar zameen par, Delhi belly, da ma wasu wadanda bamu fada ba,

3. Salman Khan.
Shima gwarzon jarumi Salman ya rera wakoki cikin Fim kamar cikin Bodyguard, Hero, da dai sauransu.

4. Shah Rukh Khan.
Wannan sanannen jarumi mai suna a kasa shi ma bai yi kasa a guiwa ba wajen rera wakoki cikin wadannan fina-finai Josh, Don2,

5 Ajay Devgan.
Wannan zakakurin jarumi mai suna a sama ya rera waka cikin Fim din Bol bhachaan,

6. Amrish Puri.
Shima wannan jarumi Amrish da aka fi Sani da mugyanbo ya rera waka cikin Fim din Tehelka,

7. Sunil Shetty.
Jarumi Sunil shima ba'a barshi baya ba domin har gidajen Radio da Takabijin yana yiwa wakoki,

8. Mithun Cakharaborty.
Jarumi Mithun ya rera waka a Fim din Ilaaka,

A bangaren maza zamu dan dakata a nan a inda zamu leka bangare mata mu kawo guda biyu kacal.


Priyanka Chopra.
A bangaren mata jaruma Kareena tana cikin masu rera waka da kan su a inda ta rera waka cikin Fim din Dil Dhadak ne Do

Alia Bhatt.
Ta rera wakoki cikin Highway, dama Finafinai da dama.

Zamu dakata a nan ba dan mun kawo karshen su ba.

Kuci gaba da bibiyar #ZaurenHausa

Monday, July 15, 2019

Bayan hutu na dogon lokaci Sunil Shetty ya dawo fagen daga

Bayan hutu na dogon lokaci Sunil Shetty ya dawo fagen daga

Ana sa ran nan ba da dadewa ba Jarumi Sunil Shetty zai dawo aiki a Bollywood bayan hutun da ya dauka na lokaci mai tsayi,

Kamar dai yadda masoyan Finafinan Bollywood dai suka sani Jarumi Sunil Shetty yana cikin shahararrun yan wasa wanda ya samu daukaka cikin fina-finain sa kamar *Balwaan* *Dildiwale* *Rakshak* *Mohra* *Bhai* da dai sauran su,
Sai dai daga baya jarumin ya fuskanci kalubale wanda hakan ya kai shi ga daukar tsawon lokaci ba tare da anji duriyar sa ba,

Sai dai ya dan leko cikin shekarar 2017 inda ya fito a matsayin Azzalumi wato "Boss" cikin wani Fim mai suna *A Gentle Man* kuma hakika masoyan sa sunyi matukar da ganin sa da suka yi domin sun yi kewar sa lokaci mai tsayi,


Albishir ga masoya Sunil Shetty shi ne a yanzu dai jarumin nasu zai dawo ko ince ya dawo wannan harka da karfin sa.

Thursday, July 11, 2019

Takaitaccen tarihin Jarumin kudancin India Allu Arjun

Takaitaccen tarihin Jarumin kudancin India Allu Arjun

A yau zamu kawo takaitaccen tarihin jarumin kafcen nan na kudancin India wato #Allun-Arjun,

Annhaifi Allu Arjun ranar 8 ga Satan afrilun 1983 a garin Hyderabad dake kasar ta India ya yi karatu a wata karamar makaranta mai suna Patric School dake grain Chennai sannan yayi karamar jami'a a garun Hyderabad,

Yana da mata 1 mai suna Sneha Reddy sun haifi 'ya'ya 2 na miji da mace mabiyin Addinin Hindu ne yana da mabiya Million 7 a shafin sa na Facebook an tambaye shi shin wane Jarumi ko Jaruma yafi so ya bada amsa da cewa Rani Mukherje.

Monday, July 8, 2019

Soyayyar Amithab Bachchan da Rekha

Soyayyar Amithab Bachchan da Rekha

A yau zamu leka fagen soyayya a Bollywood sai dai zamu yi waiwaye adon tafiya ne domin kuwa wata tsohuwar soyayya ce zamu yi magana akai,

Zamu waiga baya ne mu kawo muku wadansu abubuwa da baku sani ba game da soyayyar da jarumi Amithab Bachchan da Rekha suka yi tun shekaru aru aru da suka gabata,

Harkar fim wata abace wadda takan yi sanadiyar abubuwa daban daban takan sa wasu lalace wa saboda shuhura sannan takan hada soyayya wadda kan kai ga aure amma wani lokacin soyayyar taken kaiwa ga bakinciki ne..
Soyayyar farko wadda masana'antar fim ta Bollywood bazata taba manta wa da ita ba itace ta jarumi Amithab Bachchan da kuma jaruma Rekha wannan soyayya takai takawo matuka saidai shin zamu kirata da yaudara ne ko rashin rabo?

Wannan jarumi dai ya auri jaruma Jaya tun 1973 amma alokacin daukan wani fim dinsu DO A NJAANE wannan jarumi sun fara soyayya da jaruma wadda ake ma lakabi da Umrao jaan wato REKHA duk da shi baitaba fitowa fili ya bayyana ba amma ita REKHA bata boye komai ba...
Daga baya ma har rade radi akayi cewa sunyi aure aboye, wannan jaruma da yawa awancen lokacin sunganta da alama da ke nuna tayi aure alokacin auren RISHI KAPOOR da NEETU SINGH...
Awata hira da akayi da wannan jaruma a 1983 ta bayyana cewa Amithab na boye soyayyarsu Dan iyalin sa da kuma aikinsa amma ita tasan tanason shi kuma shima yana matukar sonta Dan haka ba wata damuwa atare da ita...
ta kara da cewa Aamith mutum ne mai halin mutanan da shi yasa bayaso ya cutar da matarsa...
Lokacin da tafara fahimtar soyayyarsu ba Inda zata sai lokacin da matarshi JAYA ta gayyaceta gidansu dansuci abincin dare anan ne take Sanar mata dacewa gwara ma kiyi hakuri domin bazan taba barmiki mijina ba kome ko zaifaru...
Ita REKHA tanason zama matar Amith amma kuma ba taso ta aureshi alhali da auran wata a kanshi....

A haka dai wannan soyayya tafara disashewa, bayan nan a 1990 tasami wani mutum ta aura amma ba Sufi wata uku ba auran yarabu sabo da ta gano yana da ciwon hauka, Wanda wannan dalilin yasa har Yau bata sake tayi aure ba sannan har yau har gobe dayawa na tunanin bata daina son Big B ba...
A wani labarin Rade radi da akayi bayan fitar fim din Silsila shine wasu naganin kamar Yash Chopra soyayyarsu ya kwaikwaya yai fim din SILSILA....
Kuma shiyasa batason suna haduwa awurin wani taro.

Saturday, July 6, 2019

Soyayyar Katrina Kaif Yadda wani matashi ya rataye kan sa

Soyayyar Katrina Kaif Yadda wani matashi ya rataye kan sa

Tsananin soyayyar Katrina Kaif ya jawo wani matashi ya yanke wa kansa hukuncin kisa sabo da ya rasa hanyar da zai bi domin samun karbuwa a wajen ta,

Wani matashi dan Jihar Mumbai dake kasar India, wanda yake karatun sa a makarantar Engeneering da ke unguwar "Indore"
ya kashe kan sa har lahira ta hanyar rataya Slsakamakon soyayyar da yake yiwa jaruma Katrina Kaif,


Shi dai matashin Saurayin ya Yanke Wannan hukuncin ne, Sakamakon Ganin duk hanyar da zai bi. Don Samun Soyayyar Katrina ya gagara,
Kasancewar ya Tura Mata Sako har Kashi Biyu, ta hanyar rubutu na Wasika. Amma kuma baiji wata Kyakykyawar Amsa daga gareta ba


Matashin Saurayin dai Mai Suna Rahul, ya kamu da tsananin son Katrina ne Wanda har ya kaishi da yanke wannan danyen hukuncin Rataye Kansa.
Fim din Sultan ya cika shekaru uku

Fim din Sultan ya cika shekaru uku

A ranar 06/07/2019 ne kasaitaccen fim dinnan na jarumi Salman Khan da Anushka Sharma wato Sultan ya cika shekaru 3 cif cif da shiga kasuwa,

Fim din da Aditya Chopra ya shirya sannan Ali Abbas Zafar ya bayar da umarni
ya Kasance kayatacce Kuma Mashahurin Shirin Jarumi Salman Khan Wanda Shi Ne Farkon Film Din Da Ya Fara Hadasu Da Fasihin Mai Bada Umarnin Nan Wato "ALI ABBAS ZAFAR". Shirin Wanda Ya Fita A Lokacin Shagulgulan Bikin karamar Sallah Wato Eid, Ya Fita Ranar Shida, Ga Watan Yuli, (July) Na Shekar "Dubu Biyu, Da Sha Shida" (2016).

Fim Din Sultan Ya Nishadantar Da Ma'abota Kallon Fina-Finan India Matuka Gaya Duba Da Yadda Jarumi Salman Khan Yayi "Suburbuda.. Sambada...!!! Mazga...!!! Hadi Da Sambade-bade...!!!"

Labarin Film Din Ya Kasance Abin Burgewa Ga Mai Kallo, Saboda Kasancewar Labarin Fim Din Ya Taba Faruwa A Zahirin Gaske. Wanda Akwai Wani "DAN DAMBE" Da Aka Taba Yi A Kasar INDIA Mai Suna "Sultan Ali Khan" Wanda Yasha Gwagwarmaya Da Gumurzu A Rayuwar sa Ta Dambe.
A Cikin Wannan Fim Munga Taurari Guda Biyu Wato...
Salman Khan A Matsayin SULTAN
Anushka Sharma A Matsayin AARFA,
.
Fim Din Sultan Labari Ne Akan Wani Bawan Allah Mai Suna Sultan Ali Khan (Salman Khan), Wanda Ya Kasance Dan Dambe Wanda Ya Ci Karo Da Kalubale Da Kuma Matsalolin Rayuwa Wanda Ya Fito Daga Wani Karamin Gari Mai Suna Haryana, Wanda Ya Kamu Da Soyayyar Wata Yarinya Mai Suna Aarfa, (Anushka Sharma) Wacce Ta Kasance 'Ya Ga Wani Malamin Koyar Da Danben Gargajiya Na Tabo, Wacce Ta Kasance Gwana A Wannan Fanni.
Amma Sai Akayi Rashin Sa'a Taki Amincewa Da Soyayyar sa Har Ma Ta Mareshi Hadi Da Jifa Da Munanan Kalamai A Gaban Abokansa Tana Hantararsa, Ganin Haka Yasa "SULTAN" Ya Jajirce, Ya Daura Damara Wajen Ganin Ya Zama 'Dan Wasan Dambe Wanda Zata Yi Alfahari Da Shi,
Sultan Ya Cimma Burinsa Ta Hanyar Aiki Tukuru Da Yayi Har Ya Zama Dan Wasan Dambe Mafi Shahara A Kasar India, Wanda Hakan Ya Bashi Damar Shiga Gasar (Olympics) Har Ya Samu Nasarar Lashe Lambar Zinare Wa Kasarsa Ta India,

Monday, July 1, 2019

Jarumai mata da basa son fim tare da Shah Rukh Khan

Jarumai mata da basa son fim tare da Shah Rukh Khan

Al'amarin mutum dan Adam a wannan rayuwa ba yadda za'ayi ka samu karbuwa a wajen kowa.
Ba yadda za'a yi kowa ya soka,

Duk kudin ka ko mulkin ka ko kyawun hallita ba zasu saka duk mutane su hadu a son ka ko kaunar ka ba,



Wannan ne dalilin da yasa duk farin jinin da Allah ya baiwa Shah Rukh Khan a duniyar Bollywood koma nace kusan duniya baki daya amma duk da haka an samu wadansu jarumai mata a Bollywood din da ko kadan basa so fim ya hado su da Jarumin,

Watakil zaku so jin sunayen kadan daga cikin wadannan jarumai mata,

To Ku boyo ni yanzu,

Jarumai mata (4) na masana'antar Fim ta Bollywood wadanda basa son yin aiki da jarumi Shah Rukh Khan,

1• Sonam kapoor

A shekaru 11 da shafe a masana'antar fim ta bollywood ta bayyana cewa bata son yin fim da Shah Rukh Khan sobo da tana ganin bambancin shekarun dake tsakaninsu,


2• Kangana ranaut

Tun ma farkon zuwan ta ta bayyana bata son yin fim da Shah Rukh Khan, ba ma shi kadai ba gaba daya khans 3 din wato Shah Rukh Khan Salman Khan Ameer Khan ba zata yi fim da su ba,


3• Ameesha patel

Itama dai irin matsalar sonam kapoor ta ambato wato bambancin shekaru.


4• Hema malini

Duk da ita ta kawo shi wannan masana'anta amma cewa ta yi Shah Rukh Khan yana wuce gona da iri a cikin fina-finansa saboda haka shi ba cikakken dan wasa ba ne,

Sunday, June 30, 2019

Jarumar Bollywood Zaira Wasim ta tuba da harkar Fim

Jarumar Bollywood Zaira Wasim ta tuba da harkar Fim

Matashiyar Jarumar Me kimanin Shekaru (18) Tayi Wata Muhimmiyar Sanarwa Me Muhimmanci da Ratsa Zuciya a Shafinta na sadarwa Inda Tayi Bayani Me Tsayi Kamar Haka.

Shekara Biyar kenan da Yankewa kaina Shawarar Shiga Wata Sabuwar Rayuwa Watau Shiga Masana'antar Shirya Film ta Bollywood Inda na Samu Shahara da Nasararo Masu Janhankali Domin nayi Amfani da Hikima da Kwazon da nake dashi da yin Duk Wani Kokari Da nake ganin Mutum ya kamata yayi Matukar Yanason kaiwa ga gaci Sedai duk ta Samun wadannan Abubuwan  Daga Yau dinnan Lahadi na bar Wannan Harkar Shirya Film Saboda a Fahimta ta Shine Akwai Abubuwan da ban jin dadinsu Sannan Barazana ne ga Addininna na Musulinci.

Taci gaba da cewa: Domin ina so na gyara Alakata da Ubangiji na.

Har ta kafa Wasu hujjoji da Ayoyin Alqur'an Sannan tace tasan Cewa WADANSU Zasu ga Rashin Kyautawarta Amma Bazata damu ba Domin Manzon Allah (S.A.W) yace Akwai Wani Lokaci da Zaizo Rikon Addini Zai Zama Kamar Riko da Garwashin wuta.
To Wannan Jaruma Tayi Films Guda Biyu Kacal Watau DANGAL da SECRET SUPERSTAR Inda Duk ta Samu Nasara Daga Cikinsu Akwai DANGAL ta Samu Gwarzuwar Me taimakawa Jaruma Ta Kasa Baki Daya (National Award for Best Suport Actress) da SECRET SUPERSTAR ta Samu Gwarzuwar Jaruma (Filmfare Award Best ActressCritics) Sannan Wata Babbar Kyauta ta Kasa watau (National Child Awards) Duk ta samesu a Kankanin Lokaci da Shigowa

Zamu iya cewa wannan ba karamin jihadi ba ne ganin cewar ta bar harkar ne a dai dai lokacin da take samun daukaka.

#bbaIndiaDala