Friday, July 12, 2019




Bello Muhammad Bello ya aske gashin kan sa kamar yadda yayi alkawari

Home › › Bello Muhammad Bello ya aske gashin kan sa kamar yadda yayi alkawari

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Idan dai masu bibiyar shafukan yanar gizo basu manta ba gabanin zaben shugaban kasar Nigeria da ya gabata sun ji yadda jarumi Bello Muhammad Bello wato General BMB ya yi alkawarin aske gashin kan sa idan idan Shugaba Buhari ya ci zabe karo na biyu,

Fitaccen jarumin ya cika alkawarin kamar yadda ya dauka wa kan sa,
A wadansu hutuna da Jarumin ya saki a shafukan sa na sada zumunta an ganshi da kwal a kwabo wanda wannan ne ke nuna lallai tabbas ya aiwatar da askin kamar yadda ya fada,
A baya dai akwai lokacin da wani ya yi masa tayin Naira dubu 500 ya aske kan sa domin ya fito a wani Fim amma yaki amince wa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.