A ranar 06/07/2019 ne kasaitaccen fim dinnan na jarumi Salman Khan da Anushka Sharma wato Sultan ya cika shekaru 3 cif cif da shiga kasuwa,
Fim din da Aditya Chopra ya shirya sannan Ali Abbas Zafar ya bayar da umarni
ya Kasance kayatacce Kuma Mashahurin Shirin Jarumi Salman Khan Wanda Shi Ne Farkon Film Din Da Ya Fara Hadasu Da Fasihin Mai Bada Umarnin Nan Wato "ALI ABBAS ZAFAR". Shirin Wanda Ya Fita A Lokacin Shagulgulan Bikin karamar Sallah Wato Eid, Ya Fita Ranar Shida, Ga Watan Yuli, (July) Na Shekar "Dubu Biyu, Da Sha Shida" (2016).
Fim Din Sultan Ya Nishadantar Da Ma'abota Kallon Fina-Finan India Matuka Gaya Duba Da Yadda Jarumi Salman Khan Yayi "Suburbuda.. Sambada...!!! Mazga...!!! Hadi Da Sambade-bade...!!!"
Labarin Film Din Ya Kasance Abin Burgewa Ga Mai Kallo, Saboda Kasancewar Labarin Fim Din Ya Taba Faruwa A Zahirin Gaske. Wanda Akwai Wani "DAN DAMBE" Da Aka Taba Yi A Kasar INDIA Mai Suna "Sultan Ali Khan" Wanda Yasha Gwagwarmaya Da Gumurzu A Rayuwar sa Ta Dambe.
A Cikin Wannan Fim Munga Taurari Guda Biyu Wato...
Salman Khan A Matsayin SULTAN
Anushka Sharma A Matsayin AARFA,
.
Fim Din Sultan Labari Ne Akan Wani Bawan Allah Mai Suna Sultan Ali Khan (Salman Khan), Wanda Ya Kasance Dan Dambe Wanda Ya Ci Karo Da Kalubale Da Kuma Matsalolin Rayuwa Wanda Ya Fito Daga Wani Karamin Gari Mai Suna Haryana, Wanda Ya Kamu Da Soyayyar Wata Yarinya Mai Suna Aarfa, (Anushka Sharma) Wacce Ta Kasance 'Ya Ga Wani Malamin Koyar Da Danben Gargajiya Na Tabo, Wacce Ta Kasance Gwana A Wannan Fanni.
Amma Sai Akayi Rashin Sa'a Taki Amincewa Da Soyayyar sa Har Ma Ta Mareshi Hadi Da Jifa Da Munanan Kalamai A Gaban Abokansa Tana Hantararsa, Ganin Haka Yasa "SULTAN" Ya Jajirce, Ya Daura Damara Wajen Ganin Ya Zama 'Dan Wasan Dambe Wanda Zata Yi Alfahari Da Shi,
Sultan Ya Cimma Burinsa Ta Hanyar Aiki Tukuru Da Yayi Har Ya Zama Dan Wasan Dambe Mafi Shahara A Kasar India, Wanda Hakan Ya Bashi Damar Shiga Gasar (Olympics) Har Ya Samu Nasarar Lashe Lambar Zinare Wa Kasarsa Ta India,
0 Comments:
Note: Only a member of this blog may post a comment.