Showing posts with label ZAUREN BOLLYWOOD. Show all posts
Showing posts with label ZAUREN BOLLYWOOD. Show all posts

Monday, October 28, 2019

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Jarumi Akshay Kumar yana daya daga cikin taurari a masana'antar Bollywood a yau zamu kawo muku wadansu cikin Faina-finan sa tare da shekaraun fitar su.

Ku biyo ni.

1: Saugandh, Ya fita a shekarar (1991)

2: Khiladi, Ya fita a shekarar (1992)

3: Waqt hamara hai, Ya fita a shekarar (1993)

4: Sainik, Ya fita a shekarar (1993)

5: Yeah dillagi, Ya fita a shekarar (1994)

6: . Main Khiladi Tu Anari. Ya fita a shekarar (1994)

7:  Mohra, Ya fita a shekarar (1994)

8: Sabse Bada Khiladi, Ya fita a shekarar (1995)

9:  Khiladiyon Ka Khiladi, Ya fita a shekarar (1996)

10: Dil To Pagal Hai, Ya fita a shekarar (1997)

11: Mr. & Mrs. Khiladi, Ya fita a shekarar (1997)

12: Sangharsh, Ya fita a shekarar (1999)

13: Jaanwar, Ya fita a shekarar (1999)


14: Hera Pheri, Ya fita a shekarar (2000)

Akshay Kumar yana da daruruwan shahararrun fina finai amma duk da haka zamu dakata a nan sai kun sake jin mu a karo na gaba.

Saturday, October 26, 2019

Friday, October 25, 2019

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

A rana mai kamar ta yau ne 25 ga Satan October auren fitattun jaruman nan na masana'antar Bollywood wato Sharukh Khan da matar sa Gauri Khan ya cika shekaru 28 cif,


An daura auren ne 25 ga watan October shekarar 1991,


Har yanzu dai masoyan biyu suna zaman su cikin koshin lafiya a matsayin ma'aurata a inda Allah ya arzuta su da 'ya'ya 3 a tsawon wadannan shekaru.

'Ya'yan nasu su ne Aryan Khan,
Suhana Khan, AbRam Khan,

A wannan karo ma masoyan sun shirya kayataccen biki tare da gayyatar 'yan uwa da abokan arziki da masoya,

Ma'auratan 2 Sharukh Khan wanda mabiyin Addinin Musulunci ne da matar sa Gauri Khan wacce ke bin Addinin Buddha sunan so ba zai taba mantuwa ba a Bollywood.

Sunday, September 29, 2019

[Bollywood]  Me kuka sani game da Amrish Puri

[Bollywood] Me kuka sani game da Amrish Puri

Me kuka sani game da Amrish Puri [Mugyambo,]


Kusan dai kamar yadda kowa ya sani jarumi "AMRISH PURI" babbar inkiyar sa wacce yayi Suhura da ita ta fannin suna a duniyar fim a nan kasar hausa itace : "MUGYAMBO",
Ga dukkan wadanda suka kasance suna bibiyar fina-finan sa sun san cewa Jarumi AMRISH PURI ko kuma ince MUGYAMBO yayi matukar kaiwa kololowa wajen iya shirya TUGGU da MAKIDA da DASISA, haka zalika ya goge sosai wajen iya shirya HIYANA da dukkan wata kitimurmura,


Baya ga haka kuma shi din shaharren mugu ne kuma azzalumi ajin farko, amma fa duk acikin duniyar fim (ba wai a duniyar azahiriyya ba),
A fagen iya acting kuwa da isar da sako yadda mai kallo zai gamsu ainun-ainun, to fah magana ta gaskiya ni dai kam a wuri na sam-sam har wa yau bashi da madadi,
Domin kuwa kusan dukkanin kafatanin rubunan fina-finan sa babu na yarwa, matukar ka ganshi acikin fim to ka kalla kawai, domin baya hawa fim marar ma'ana,

Na kalli tarin tulin fina-finan sa masu yawan gaske, fim dinsa na farko da na fara kalla shi ne fim din "GHAYAL", na kalli fim din shekaru kusan 21 da suka shu'de ranar lahadi da misalin karfe 11:15
Daga nan kuma sai irinsu

- GATAK,
- SALAAKHEN,
- JEET,
- KOYLA,
- LOHA,
- DAMINI,
- DILWALE DIL HANIYALE JAYENGE
- BADAL, etc,

Nasan cewa wanda duk ya kalli wadannan fina-finan dana lissafo lallai zai amintu da batutuwan da na zayyano game da wannan  Jarumin mai suna "AMRISH PURI" wato MUGYAMBO,
Malam MUGYAMBO akwai kurari da muzurai da nuna isa da tumbatsa, da kuma barazana, amma fa idan akwai basawan a kusa dashi, idan kuwa basawa suka kare to fah baya kasala wajen arar kafar Kare matsera.


Tuesday, September 17, 2019

Jarumai mabiya adinnin Hindu da suka auri mata Musulmai a Bollywood

Jarumai mabiya adinnin Hindu da suka auri mata Musulmai a Bollywood

A yau muna dauke da sunayen wadansu shahararrun jaruman Bollywood wadanda ba Musulmai ba amma sun auri mata Musulmai,

Ga sunayen ma'auratan kamar haka..,

1: Sanjay Duty ya auri Manyata Dutt a ranar 7 ga watan February na shekarar 2008 asalin sunan ta shi ne Sarah Khan Musulma ce ta haifa masa 'yan biyu mace da namiji,

2: Hrithik Roshan ya auri Sussanne Khan ranar 20 ga watan December shekarar 2000 sun rabu a 2014 sun haifi 'ya'ya biyu,

3: Sunil Shetty ya auri Mana Qadri a shekarar 1991 Allah ya azurta su da 'ya'ya biyu,

4: Aditya Pancholi ya auri Zarina Wahab a shekarar 1986 suma sun haifi 'ya'ya biyu ne,

5: Atul Agnihotri ya auri Alvira Khan cikin shekarar 1996,

A takaice wadannan su ne jerin jarumai maza wadanda ba musulmai ba amma sun auri mata Musulmai a Bollywood.

Muna fatan Allah ya tsare mana imanin mu.


Monday, July 22, 2019

Manyan jaruman Bollywood kuma mawaka

Manyan jaruman Bollywood kuma mawaka

A yau zamu kawo muku jerin sunayen wadansu jaruman fim na kasar India da suka taba rera wakar Fim da kan su,

Ba tare da bata lokaci ba ga jerangiyar jaruman #Bollywood da suka rera wakoki da kan su

1. Amitabh Bachchan,
Wannan sanannan tsohon jarumin mazan jiya ya rera waka da kan sa cikin Fina-finai kamar haka. Silsila, Toofan, Baghbaan, Baabul, da dai sauran su wato bama sau daya ne ya rera waka ba,

2. Amir Khan.
Wannan jarumi mai suna a sama shima ya rera wakoki da dama cikin Finafinai kamar Ghulam, Dangal, Taar zameen par, Delhi belly, da ma wasu wadanda bamu fada ba,

3. Salman Khan.
Shima gwarzon jarumi Salman ya rera wakoki cikin Fim kamar cikin Bodyguard, Hero, da dai sauransu.

4. Shah Rukh Khan.
Wannan sanannen jarumi mai suna a kasa shi ma bai yi kasa a guiwa ba wajen rera wakoki cikin wadannan fina-finai Josh, Don2,

5 Ajay Devgan.
Wannan zakakurin jarumi mai suna a sama ya rera waka cikin Fim din Bol bhachaan,

6. Amrish Puri.
Shima wannan jarumi Amrish da aka fi Sani da mugyanbo ya rera waka cikin Fim din Tehelka,

7. Sunil Shetty.
Jarumi Sunil shima ba'a barshi baya ba domin har gidajen Radio da Takabijin yana yiwa wakoki,

8. Mithun Cakharaborty.
Jarumi Mithun ya rera waka a Fim din Ilaaka,

A bangaren maza zamu dan dakata a nan a inda zamu leka bangare mata mu kawo guda biyu kacal.


Priyanka Chopra.
A bangaren mata jaruma Kareena tana cikin masu rera waka da kan su a inda ta rera waka cikin Fim din Dil Dhadak ne Do

Alia Bhatt.
Ta rera wakoki cikin Highway, dama Finafinai da dama.

Zamu dakata a nan ba dan mun kawo karshen su ba.

Kuci gaba da bibiyar #ZaurenHausa

Monday, July 15, 2019

Bayan hutu na dogon lokaci Sunil Shetty ya dawo fagen daga

Bayan hutu na dogon lokaci Sunil Shetty ya dawo fagen daga

Ana sa ran nan ba da dadewa ba Jarumi Sunil Shetty zai dawo aiki a Bollywood bayan hutun da ya dauka na lokaci mai tsayi,

Kamar dai yadda masoyan Finafinan Bollywood dai suka sani Jarumi Sunil Shetty yana cikin shahararrun yan wasa wanda ya samu daukaka cikin fina-finain sa kamar *Balwaan* *Dildiwale* *Rakshak* *Mohra* *Bhai* da dai sauran su,
Sai dai daga baya jarumin ya fuskanci kalubale wanda hakan ya kai shi ga daukar tsawon lokaci ba tare da anji duriyar sa ba,

Sai dai ya dan leko cikin shekarar 2017 inda ya fito a matsayin Azzalumi wato "Boss" cikin wani Fim mai suna *A Gentle Man* kuma hakika masoyan sa sunyi matukar da ganin sa da suka yi domin sun yi kewar sa lokaci mai tsayi,


Albishir ga masoya Sunil Shetty shi ne a yanzu dai jarumin nasu zai dawo ko ince ya dawo wannan harka da karfin sa.