Friday, August 30, 2019




WASIKAR MALAM IBRAHIM SHEKARAU GA GWAMNAN RIBAS

Home WASIKAR MALAM IBRAHIM SHEKARAU GA GWAMNAN RIBAS

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Tsohon gwamnan jihar kano kuma sanatan kano ta tsakiya a yanzu mai girma Malam Ibrahim Shekarau ya aike da Damon mayar da martani ga gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike dangane da rushe Masallacin Juma'a da aka yi a jihar sa,

Dardaunan na Kano yayi kira da babbar murya ga yan Nigeria da suyi Allah wadai da abun da gwamnan Ribas na rushe wurin ibadar Musulmai dake a unguwar Trans Amadi babban birnin Fatakwal
A inda ya ci gaba da cewa munji gwamnan Ribas yayi alwashin ba zai bada hakuri game da abun da ya aiwatar ba wanda hakan rashin adalci ne da kuma ganganci da ma yunkurin tayar da husuma cikin kasa, "

Yanzu idan aka samu wani gwamna Musulmi ya ayyana jihar sa a matsayin jihar Musulmai zalla sannan ya rika bi yana rushe coci coci zaka ji duniya ta yi ca akan hakan kuma mabiya Addinin kirista zasu nemi agajin kungiyoyi na kasashen duniya har ma da majalisar dinkin duniya,

Haka ma da wani gwamna Musulmi zai furta munanan kalamai game da kirista kwatankwacin na gwamna Wike to da hakan zai girgiza Nigeria ta yadda zai jawo mabiya Addinin kirista su yi ca a kan sa sai dai abun takaici munga wasu shuwagabannin kirista na wannan kasa suna goyon bayan abun da gwamnan Rivas ya aikata inji Malam Shekarau

Yaci gaba da cewa Nigeria kasarmu ce gaba daya babu wata jiha da ke da ikon ayyana wani Addini kwaya daya a matsayin Addinin ta sanin darajar shugabanci shi ne ka rungumi kowa naka ne,

Idan za'a iya tuna wa lokacin da na zama gwamnan jihar Kano daga Shekarau 2003 zuwa 2011 mun karfafa mutane da su gudanar da rayuwar su a bisa tsarin shari'ar Musulunci amma hakan bai sa mun yi amfani da wannan dama wajen rushe wajen ibadar kiristoci ba,"
sannan ba mu yi amfani da damar da tsarin Mulkin kasa na kwansitushin sashi na 10 da ya bamu ikon ayyana jihar Kano a matsayin jihar Musulunci ba..

Abinda muka yiwa jama'ar Kano na adalci hakan ya jawo an yabe mu, mun samu yabo hatta daga kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) reshen jihar Kano a lokuta da dama, wadannan shugabannin kiristoci da suka yabemu har yanzu suna raye, zasu iya tabbatar da abinda nake fadi, ya kamata gwamnan jihar Rivers ya san da cewa; Mr Tala Ilo daga jihar Bayelsa da Mr. Chris Chibuzor Azuka daga jihar Anambra dukkansu mabiya addinin kirista ne, amma sun kasance daga cikin masu bani shawara na musamman lokacin da nake gwamnan jihar Kano...


Nyesom Wike yayi alwashin cewa Rivers jihar kiristoci ne zalla, wannan zancen banza ne da rashin hankali, ba dukkan mutanen dake Rivers ne mabiya addinin kirista ba, ba daidai bane jihar Rivera ta zama na kiristoci zalla kamar yadda ba daidai bane ace musulmai da sauran mabiya addini da suka fito daga sassan Nigeria su dauki jihar Rivers a matsayin jihar su su kadai ba, sannan Nyesom Wike yana gudanar da jihar Rivers bisa tsari na dokoki wanda ba irin na gwamnatin Nigeria ba, wannan ya nuna mana gwamnatin Rivers bata dauki wasu daga cikin manyan jiga jiganta musulmai 'yan asalin jihar ba a matsayin 'yan jihar Rivers, saboda kasancewarsu musulmai, irinsu Alabo Mujahid Dokubo Asari, Alhaji Isa Boaima, Alhaji Sani Okiri, Alhaji Ahmed Sani Pe, Alhaji Abdul’aziz Pepple, Alhaji Sulaiman Akani, Alhaji Ibrahim Orlu, Alhaji Musa Brown, Chief Hassan Douglas da Alhaji Mustapha Wakama
Sardaunan Kano yaci gaba da cewa; Ba wannan bane karo na farko da gwamnan Rivers Nyesom Wike yake bayyana wautarsa da rashin hankali ba, idan za'a tuna shekaran da ta gabata, yayi barazanan cewa zai rushe shugabancin jam'iyyarsa ta PDP idan har sukaki gudanar da babban taron jam'iyyar a birnin Fatajwal jihar Ribas, abin mamaki kuma sai suka biye wa wannan marar mutunci suka je suka gudanar da taron a inda ya bukata

Matakin da gwamnan Rivers yake dauka da irin munanan kalmomin da yake furtawa yana bayyana irin mutanen da basu cancanta ace sune jagororin al'umma ba, abinda yakeyi kokari ne wajen wargaza tsarin mulkin demokaradiyya a wannan kasa, sannan babban barazana ne da kalubale wa zaman lafiyar kasa, don haka muna kira ga gwamnatin Nigeria da dukkan hukumomin tsaron Nigeria da su fadakar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, sannan a tabbatar mishi da cewa idan ya kuskura ya kunna wutar rikici a Kasar zai girbi sakamakon abinda ya aikata
Daga karshe, ina kira ga musulmai mazauna jihar Rivers da dukkan Musulmai a Nigeria gaba daya da su kwantar da hankali, sannan su kasance masu da'a da bin doka, kar mu kwaikwayi mummunan dabi'a na Nyesom Wike, a cikin 'yan uwansa kiristoci akwai mutanen kirki masu son zaman lafiya, kar mu bari hankali da tunaninmu ya gushe mu je mu aikata ba daidai ba, kamata yayi mu karfafi 'yan uwanmu musulmai na jihar Rivers da su tsaya akan imaninsu, su mayar da hankali wajen bin matakin doka a kotu su kwato hakkinsu kamar yadda suka taba yin haka a baya, wannan karon zasu bukaci a sake gina musu Masallacin da aka rushe a Trans-Amadi, sannan a biya diyyah, bayan haka su bukaci gwamna Nyesom Wike ya fito ya bada hakuri wa 'yan Nigeria.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.