Sunday, September 1, 2019




YADDA AKE GYARA FATA DA LEMON TSAMI

Home YADDA AKE GYARA FATA DA LEMON TSAMI

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Masu bibiyar wannan shafi namu na ZaurenHausa barkan mu da sake saduwa a dai dai wannan lokaci,

Da yardar Ubangiji a yau zamu yi takaitaccen bayani ne game da yadda ake amfani da lemon tsami wajen gyaran fuska ta dawo mai sheki da haske da kyau abun burgewa..

Ganin yadda a yanzu kannin mu da yayyen mu yan mata sun mayar da hankalin su wajen amfani da mayuka da ke zuwa daga kasashen waje wajen gyara fuskokin su wanda sau da dama haka yana da matukar illa a tare da su shi yasa na yanke shawarar gabatar da wannan takaitaccen bayani domin amfanin mu baki days,

Ba tare da bata lokaci ba ku biyo ni

Yadda zaki gyara fuskar ki ta hanyar amfani da lemon tsami ta yadda fuskar ki zata yi sheki fari kyau da dai sauran su yi amfani da wannan

Abubuwan da ake bukata

1" Lemon tsami guda biyu

2" Madara Peak Milk sashet biyu

"3 Dan karamin muzubi

Bayani kin samu wadannan abubuwan da na zayyano a sama sai ki samu wuka ki yanka lemon tsamin a biyu ki matse ruwan sa gaba daya cikin mazubi bayan kin gama wannan sai ki bude madarar ki zuba cikin ruwan lemon ki garwaya su hadu sosai sai ki rufe ki samu ruwa mai kyau ki wanke fuskar ki da kyau ki samu tsumma ki guge fuskar sosai sai ki rika debo wannan hadi na lemo da madara kina Shafa wa a fuskar ki ko ina a hankali amma a kiyaye ido bayan kin gama sai ki jira a kalla mintuna 15 bayan nan sai ki samu ruwan zafi ki wanke fuskar ki,

Idan kika gwada wannan kamar kwanaki uku zaki sha mamaki kuma baya cutar wa ko kadan bayan haka ko kusa baya kama da mayuka na blicin da mata ke amfani da shi a yau

Zaki ci gaba da yi lokaci bayan lokaci.

Zan dakata a nan

Kuci gaba da kasancewa da ZaurenHausa



WhatsApp +2347065220089

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.