Showing posts with label ZAUREN KIMIYYA. Show all posts
Showing posts with label ZAUREN KIMIYYA. Show all posts

Sunday, September 22, 2019

Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Akwai mutane da yawa da suka fada hannun mazambata sabo da basa iya tantance takardar kudi ta kwarai da ta jabu wanda dalilin hakan suka tafka hasara wannan dalili ne ya sa a yau zamu kawo muku wadansu hanyoyi da masana suka fito da su game da yadda zaka iya banbance kudin jabu wato (Fake Money)

Ku biyo mu,

1> Shafa
Hanya ta farko da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne rike wa a hannu ka shafa idan ka ji ta fiye laushi kamar takarda to kudin jabu ne kada ka karba..,

2>Ruwa
Hanya ta biyu da zaka gane kudin jabu shi ne ka jika hannun ka da ruwa sannan ka shafi takardar kidin idan kaga kalar su ta fara wanke wa to kada ka karba na jabu ne
Haka ma zaka iya samun ruwa ka saka kudin a ciki kimanin sakan 30 da zaran kaga launin kudin ya fara canza ruwan to hakan na nufin jabu ne..,

3>Hatimi
Hanya ta uku da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne akwai wani hatimi a jikin Naira 1000 mai launin gwal to idan jabun kudi ne ka gwada kankare wannan hatimi da hannun ka zaka ga ya wuce..,

4>Zare
Hanya ta hudu da zaka iya gane jabun kudi shi ne ko wane takardar kudi akwai wani zare mai sheki yana da tsayi dai dai da takardar kudin yana da dan kauri yadda hannu zai iya jin sa ya fi bayyana a tsofoffin takardun kudi to idan jabun kudi ne zaka ga zaren bashi da kauri sosai kamar na kudin kwarai sannan yana da saurin kankaruwa da zaka gwada..,

5>Haske
Hanya ta biyar da zaka iya gane jabun kudi shi ne amfani da kwan lantarki mai dauke da sinadarin MERCURY akwai wasu abubuwa jikin takardar kudi da ido baya iya ganin su ba tare da taimakon hasken wutar lantarki mai dauke da MERCURY ba wanda ko wacce takardar Naira na dauke da su
Idan kayi amfani da wannan hanya ka duba takardar Naira 1000 da kwan wutar lantarki zaka ga an rubuta 1,000 da lambobi kwance a jikin takardar wanda idan kudin jabu ne zai ga abun a juye ne (UPSIDE DOWN).

Akwai hanyoyi da dama da ake gane jabun kudi amma wannan su ne masu sauki wadanda kowa ma zai iya.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuci gaba da kasancewa da Zaurenhausa.com

Sannan kuyi share zuwa yan uwa da abokan arziki domin su amfana.

Thursday, September 19, 2019

Yadda ake sauraron kiran wayar ka

Yadda ake sauraron kiran wayar ka

Ko kasan da cewa zai iya kasancewa duk kiran wayar da kake yi akwai wani yana nan yana sauraron ka ba tare da ka Sani ba?

Biyo ni


A kwai hanyoyi da dama da mutane zasu iya amfani da ita wajen hade wayar su da taka yadda zai zamo duk lokacin da ka yi kira ko aka kira ka zai rika sauraron firar da kuke yi
Hakika wannan abu ne mai sauki a wannan zamani da ci gaba ya zagaye ko ina,

Amma hanya mai sauki ita ce ta hanyar da za'a karbi wayar ka ka Sani ko baka sani ba a danna lambobi a hada wannan abu,

Samari zasu iya amfani da wannan dama wajen sauraron wayar da budurwar su ke yi da wadansu samarin ta,

Abokai zasu iya hada maka wannan abu a waya ya kasance a duk lokacin da ka kira ko aka kira ka wani ya rika sauraro,

Yadda zaka gano shin an hada maka wannan abu ko aa danna wanna *#61# nan take zaka ga lambar da ake sauraron kiran wayar ka da ita,

Domin cire wannan tsari danna ##002# nan take zaka yi waje da mai sauraron kiran wayar ka,


Yana da kyau lokaci bayan lokaci ka rika danna wannan din ##002# domin cire wa idan ma an hada.

Kuyi share zuwa kafofin sadarwa domin wadansu su amfana.



Sunday, September 1, 2019

YADDA AKE GYARA FATA DA LEMON TSAMI

YADDA AKE GYARA FATA DA LEMON TSAMI

Masu bibiyar wannan shafi namu na ZaurenHausa barkan mu da sake saduwa a dai dai wannan lokaci,

Da yardar Ubangiji a yau zamu yi takaitaccen bayani ne game da yadda ake amfani da lemon tsami wajen gyaran fuska ta dawo mai sheki da haske da kyau abun burgewa..

Ganin yadda a yanzu kannin mu da yayyen mu yan mata sun mayar da hankalin su wajen amfani da mayuka da ke zuwa daga kasashen waje wajen gyara fuskokin su wanda sau da dama haka yana da matukar illa a tare da su shi yasa na yanke shawarar gabatar da wannan takaitaccen bayani domin amfanin mu baki days,

Ba tare da bata lokaci ba ku biyo ni

Yadda zaki gyara fuskar ki ta hanyar amfani da lemon tsami ta yadda fuskar ki zata yi sheki fari kyau da dai sauran su yi amfani da wannan

Abubuwan da ake bukata

1" Lemon tsami guda biyu

2" Madara Peak Milk sashet biyu

"3 Dan karamin muzubi

Bayani kin samu wadannan abubuwan da na zayyano a sama sai ki samu wuka ki yanka lemon tsamin a biyu ki matse ruwan sa gaba daya cikin mazubi bayan kin gama wannan sai ki bude madarar ki zuba cikin ruwan lemon ki garwaya su hadu sosai sai ki rufe ki samu ruwa mai kyau ki wanke fuskar ki da kyau ki samu tsumma ki guge fuskar sosai sai ki rika debo wannan hadi na lemo da madara kina Shafa wa a fuskar ki ko ina a hankali amma a kiyaye ido bayan kin gama sai ki jira a kalla mintuna 15 bayan nan sai ki samu ruwan zafi ki wanke fuskar ki,

Idan kika gwada wannan kamar kwanaki uku zaki sha mamaki kuma baya cutar wa ko kadan bayan haka ko kusa baya kama da mayuka na blicin da mata ke amfani da shi a yau

Zaki ci gaba da yi lokaci bayan lokaci.

Zan dakata a nan

Kuci gaba da kasancewa da ZaurenHausa



WhatsApp +2347065220089