A kwanakin nan da suka gabata ne dai al'umar Musulmai mazauna babban birnin fatakal a jihar ribas suka yi korfi dangane da yadda gomnatin jihar ta rushed musu Masallacin su na Juma'a,
Sai dai rushe wannan masallaci ya jawo cece kuce bama a fatakwal ma har ma Nigeria baki daya a inda hakan ya jawo gwamnan jihar Nyesok Wike ya fito yana karyata wannan batu da cewa: babu wani Masallaci a wannan wuri da ake fada har ta kai shi ga jagorantar tawagar yan jarida zuwa wajen yana fadar a nuna masa wajen da aka rushe Masallacin"
To sai dai abu ne sananne cewa tabbas akwai ginin masallaci a wurin da ake magana, kuma takaddama a kan filin masallacin ta faro ne tun zamanin Gwamna Rotimi Amaechi kamar yadda wani dan kwamitin masallacin ya fada,
A inda yake cewa tun a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ne suka fara samun matsala wadda ta kai su ga zuwa kotu. “Amma a wannan mulki na Nyesom Wike babu wata matsala a tsakaninmu da za a ce ita ce musabbanin rushe masallacin akwai lokacin da muka taba fuskantar matsala a gwamnatin Ameachi. Mun sayi wurin lafiya lau da aka sa ginshikin gini da tubuli sai gwamnatin Ameachi ta turo aka rushe bisa cewa ba mu saye shi kan ka’ida ba. Muka shigar da kara aka yi shari’a kotu ta ba mu gaskiya. Ba mu ne asalin masu kara ba wanda ya sayar mana da filin ne ya kai karar gwamnati, kuma kotu ta ba shi gaskiya sannan aka tabbatar mana cewa muna da izinin yin abin da muka ga dama da filinmu. Gwamnati ta sake daukaka kara, kara iri biyu ce akwai ta rushe mana masallaci sannan akwai ta hana gwamnati kada ta karbe mana fili, kuma muna bukatar gwamnati ta mayar mana da asarar da muka yi saboda ta rushe mana wuri ba bisa ka’ida ba. To waccan gwamnati ta wuce, wannan kuma ba mu da wata matsala da ita. Gwamnatin Nyesom Wike ce ma ta janye karar ta ce ba ta bukatar a ci gaba da shari’ar wannan lamari, kuma hakan shi ya ba mu dama muka ce, bari mu je mu sasanta da ’yan asalin wurin domin mu ci gaba da aikinmu,”inji shi"
Yaci gaba da cew a nasu tunanin ba wata matsala a tsakaninsu da gwamnatin Wike face nuna wa Musulunci kyama da kin jinin Musulmi da Gwamna yake yi “Wannan shi ne dalili kuma fahimtarmu, wannan ba zai rasa nasaba da kin Musulunci ba tunda Gwamnan kullum yana ikirari jiharsa jiha ce ta addinin Kirista dari-bisa dari"
Kafin rushe mana wannan Masallaci babu wani sako na baka ko a rubuce da gwamnati ta aiko mana kan za ta rushe masallacin “Babu takarda illa wani lokaci sun zo suka ci mana zarafi suka tafi suka cire mana kwanon rufi da muka sayo suka tafi sai muka dauki takardunmu muka tafi Ma’aikatar Filaye da Muhalli ta Jihar Ribas, muka nuna musu suka duba suka ce tabbas lallai mun bi ka’ida suka rubuta mana takardar amincewa mu ci gaba da gininmu bisa damar da Gwamnatin Jihar Ribas ta ba mu,”
Ya ci gaba da cewa, yanzu bamu dauki wani matakin zuwa kotu ba tukun amma muna nan muna daukar matakan tuntuba, domin ba ma son tashin hanakali, “Muna bukatar zaman lafiya kuma mu masu yin biyayya ne ga gwamnati amma muna bin matakin da ya dace, nan gaba za mu san cewa za mu tafi kotu ko a’a. Amma yanzu muna bin matakan tuntubar dattawa da wadanda suka dace tunda abu ne na addini,” inji shi.
Ya ce an kai shekara 10 ana gudanar da ibada a cikin masallacin “Akwai wani wuri da ake kira Rambo Billage, wannan kauye tsohon bariki ne na sojoji, to akwai mutanenmu a wurin suna Sallah. Lokacin da ake Sallah a wurin sai wannan ya fito da wannan fili zai sayar shi ne mutane suka yi hobbasa suka ce maimakon a rasa wannan dama me ya sa ba za a sayi wannan fili a gina Masallacin Juma’a ba, saboda mun duba mun ga duk Trans-Amadi babu masallacin da za a yi Sallar Juma’a. Mun fara ginin masallacin akalla tun shekarar 2012,” inji shi.
Sai dai Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya karyata batun rusa masallacin inda ya ce makiya son zaman lafiya ne suka kitsa labari suke bazawa a sako da lungun jihar. Gwamnan ya karyata batun ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya jagoranci ayarin ’yan jarida zuwa harabar masallacin da ake zarginsa da bada umarnin a rushe shi. Ya ce “Babu wani masallaci da aka rushe tunda ban ga komai ba.” Ya ce “An sha kirana ta waya daga sassa daban-daban na kasar nan, manyan mutane sai buga min waya suke ta yi game da batun masallacin. Ni a iya sanina wadansu mutane ne suka zo nan suka fara yin gine-gine ba bisa ka’ida ba, babu izinin hukuma ko gwamnatin jiha wanda ya fara yin gini a wurin ya kai karar gwamnati.”
Daga nan sai ya kalubalanci al’ummar Musulmin jihar su zo su nuna masa inda aka rushe masallacin, ya ce akwai masallatai masu yawan gaske a jihar da aka gina su bisa izinin gwamnati yaya ba a rusa su ba? Ya ce wancan wuri wadansu ne suka fara yin gini ba kan ka’ida ba hukuma tazo ta hana su ta dakatar da su, sai ya yi tambayat “Mece ce ribarmu idan muka rushe masallaci alhali ana da masallatai masu yawa a jihar nan?
Sai dai a nasa bangaren Limamin Masallacin Juma’ar na Trans-Amadi da ake takaddama, Imam Haroon Muhammad ya ce tabbas akwai masallaci a wurin, inda ya ce lokacin da gwamnatin ta rushe masallacin a gurguje suka rika kwashe baraguzan ginin masallacin suna tafiya da su. Ya ce hatta ginshikan masallacin nasu guda 108 sun kwashe su, “Komai kwashe shi suka yi ba mu san inda suka kai ba. Zuwa suka yi da motar rushe gini suka ture ginin suka tafi da komai na masallacin da kansu,”
Imam Haroon Muhammad, ya ce ba zai iya kiran Gwamnan da makaryaci ba, amma da akwai masallaci a wurin “Ba zan iya kiransa makaryaci ba, amma akwai masallaci a wurin sai dai idan mukaraban sa ne suka yi masa karya suka gaya masa karya. Masu rushe masallacin sun zo ne da motar rushe gine-gine, kuma suna rushe ginin suka kwashe baraguzan sa, kila sun yi haka ne don kawar da duk wata shaida. Kuma kila shi ya sa Gwamnan ya bugu kirjin a zo a nuna masa alamar rushe gini a wurin,”
Limamin ya ci gaba da cewa tun wajen karshen shekarar 2008 zuwa farko-farkon 2009 suka gyara wurin suka fara Sallah a wurin. “Idan da a ce ka san wurin akwai korama da ta ratsa wurin mu ne muka yi aikin gyara ta, muka fitar da hanya mun kashe wajen Naira miliyan takwas kan aikin, mun killace wurin tun shekarar 2008, a karshe-karshenta muka fara Sallah a wurin bayan mun gyara shi,
Imam Haroon Muhammad ya tabbatar wa Aminiya cewa an yi shari’a a kotu a tsakanin wannan masallacin da gwamnatin jihar inda ya ce a wancan lokaci kotu ta yanke hukuncin cewa dakatar da Musulmi daga gina masallacin kuskure ne a kyale musu filinsu. “Suna so ne kotu ta ce ga wani a matsayin mai fili a kwace mana shi, ita kuma kotu ta ce a’a. Bayan shekara bakwai ko takwas sai suka yi watsi da kotun suka guje mata suka daina ma halartar wajen shari’ar. Shi kuma alkalin kotun ya nemi su zo da suka zo sai ya ce su janye karar aka kori karar,” inji Limamin.
Imam Haroon Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa an yi shari’ar ce a gaban Babbar Kotun Jihar ta 4 a karkashin Mai shari’a Bomadi Preye.
Imama Haroon ya ce ba su iya cewa ga adadin Musulmin da suke Sallah a masallacin, tunda ba rajistar masu Sallah ake yi a masallatai ba. “Ka san masallaci ba ya rajistar masallata, amma fiye da mutum 2000 kowace Juma’a suke zuwa yin Sallah, haka muke cika wurin da jama’a. Shi ne masallaci mafi daukar yawan jama’a a Fatakwal, kai bari ma in ce maka duk Jihar Ribas kwata babu kamarsa,” inji Limamin.
Tuni daidaikun mutane da kungiyoyin addini da na kare hakkin jama’a suka soki wannan mataki na rushe masallacin.
A martanin da Kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta mayar ta la’anci wannan mataki na Gwamnatin Jihar Ribas, inda ta bayyana cewa ’yan banga ne kawai suke gudanar da Gidan Gwamnatin Jihar.
Shugaban Kungiyar MURIC, Farfesa Ishak Kulle Sani ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce rushe masallacin wani yunkuri ne na takalar al’ummar Musulmi da kuma neman tayar da zaune-tsaye.
0 Comments:
Note: Only a member of this blog may post a comment.