Friday, August 2, 2019




Ana siyasantar da batun Alzakzaky Sheikh Bala Lau

Home Ana siyasantar da batun Alzakzaky Sheikh Bala Lau

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
A dai dai lokacin da yake gabatar da hudubar Juma'a shugaban kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'a Wa Iqamatus Sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau Yayi Kira ga gwamnatin Nigeria ta yiwa Sheikh  Alzakzaky adalci.
Shehin malamin Addinin yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar da hudubar Juma'a a Masallacin JIBWIS da ke unguwar Utaku a Abuja
Ba wannan ne karo na farko da Malam Bala Lau ke magana game da batun Malam Zakzaky ba,
Idan ba a manta ba a baya ma Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa ya duba batun Malam Zakzaky kuma yana da kyau ya sallameshi" Sheikh Bala Lau yaci gaba da cewa ko kafiri ne yayi ba dai dai ba a hukunta shi amma ayi masa adakci,


Ya ci gaba da cewa: "Idan ba a yi masa hukunci ba zanga-zanga da tawaye za su sa a sake shi. Idan kuwa aka sake shi to ranar da duk aka kama wani shugaba na kowane addini mabiyansa su ma su fito su yi zanga-zanga, su yi abin da suka ga dama domin a saki shugabansu.
"Daga nan babu sauran zaman lafiya kenan," in ji shi.

Ya ce: idan idan an tabbatar jagoran mabiya Shi'a din bai aikata laifi ba to kawai a sake shi idan kuma laifi ya aikata to ayi masa hukunci na adakci kamar ko wane cikakken dan kasa haka ne zai kawo wa kasa zaman lafiya mai dore wa."
Hakika bana jin dadin yadda wadansu mutane ke siyasantar da batun nan" domin akwai masu kokarin amfani da wannan batu domin hada fitina a wannan kasa ta hanyar cewa idan aka gama da yan Shi'a za'a dawo kan yan darika ne kuma wannan ba dai dai ba ne magana ce da zata iya haifar da tashin hankali wanda muna fatan Allah ya tsare,"
Ya kara da cewa 'yan darika sun fi kusa da 'yan Izala fiye da kusancin su da 'yan shi'a.
Da ya dawo batun rahoton BBC dangane da Muhammad Yusuf Shehin Malamin Bala Lau cewa yayi hakika #BBC tayi kuskure da ta danganta tsohon shugaban kungiyar Boko Haram din da cewa yayi karatu a Jami'ar Musulunci dake Madina,
Labarin an wallafa shi ne saboda cika shekara 10 da aka yi da fara rikicin Boko Haram a Najeriya.
Sheikh Bala Lau ya yi kira ga BBC din da ta gaggauta gyara kuskuren da ta yi.
Sai dai tuni BBC ta gyara wannan kuskure 'yan sa'o'i bayan wallafa labarin kuma ta nemi gafar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.