Matashiyar Jarumar Me kimanin Shekaru (18) Tayi Wata Muhimmiyar Sanarwa Me Muhimmanci da Ratsa Zuciya a Shafinta na sadarwa Inda Tayi Bayani Me Tsayi Kamar Haka.
Shekara Biyar kenan da Yankewa kaina Shawarar Shiga Wata Sabuwar Rayuwa Watau Shiga Masana'antar Shirya Film ta Bollywood Inda na Samu Shahara da Nasararo Masu Janhankali Domin nayi Amfani da Hikima da Kwazon da nake dashi da yin Duk Wani Kokari Da nake ganin Mutum ya kamata yayi Matukar Yanason kaiwa ga gaci Sedai duk ta Samun wadannan Abubuwan Daga Yau dinnan Lahadi na bar Wannan Harkar Shirya Film Saboda a Fahimta ta Shine Akwai Abubuwan da ban jin dadinsu Sannan Barazana ne ga Addininna na Musulinci.
Taci gaba da cewa: Domin ina so na gyara Alakata da Ubangiji na.
Har ta kafa Wasu hujjoji da Ayoyin Alqur'an Sannan tace tasan Cewa WADANSU Zasu ga Rashin Kyautawarta Amma Bazata damu ba Domin Manzon Allah (S.A.W) yace Akwai Wani Lokaci da Zaizo Rikon Addini Zai Zama Kamar Riko da Garwashin wuta.
To Wannan Jaruma Tayi Films Guda Biyu Kacal Watau DANGAL da SECRET SUPERSTAR Inda Duk ta Samu Nasara Daga Cikinsu Akwai DANGAL ta Samu Gwarzuwar Me taimakawa Jaruma Ta Kasa Baki Daya (National Award for Best Suport Actress) da SECRET SUPERSTAR ta Samu Gwarzuwar Jaruma (Filmfare Award Best ActressCritics) Sannan Wata Babbar Kyauta ta Kasa watau (National Child Awards) Duk ta samesu a Kankanin Lokaci da Shigowa
Zamu iya cewa wannan ba karamin jihadi ba ne ganin cewar ta bar harkar ne a dai dai lokacin da take samun daukaka.
#bbaIndiaDala
0 Comments:
Note: Only a member of this blog may post a comment.