Sunday, June 30, 2019




Mutuwar Kumurci jita jita ce kawai

Home Mutuwar Kumurci jita jita ce kawai

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Kamar dai yadda kowa ya sani ba wannan ne karo na farko da ake yada jita jitar mutuwa ga yan fim ba.

Kai bama yan fim ba ma ana yada irin wannan jita jita ta mutuwa ga duk wani mutum da yayi suna a kasa ko duniya baki daya

Misali zaka samu anyi irin wannan ga Malaman Addini ko yan siyasa ko mawaka kai har da yan kwallon faka.

Irin wannan jita jitar ce dai tayi ta yaduwa cewar wai jarumin fina-finan Hausa na kannywood shu'ibu lawal da aka sani da kumurci ya rasu to sai dai a wannan karon ma karya ce zunzurutu da wani ya zauna ya tsara da wata manufa da shi ne ya san ta

Alhaji Shu'ibu Lawal dai yana nan cikin koshin lafiya kamar yadda ya fito ya bayyana da bakin sa.


A wani video da ya bayyana tare da dan aura da suka dora a shafin Instagram jarumi Shu'ibu Lawal ya ce masu fatan mutuwa ta kuyi hakuri lokacin yana nan zuwa ko ku riga mu ko mu riga ku" kamar yadda yace:

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.