Saturday, July 27, 2019




Yan mata Sun fake da Fim ne suna neman maza Tanimu Akawu

Home Yan mata Sun fake da Fim ne suna neman maza Tanimu Akawu

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Daya daga cikin dattijai na masana'antar Fim ta Kannywood ya yi hira da manema labarai a inda ya fallasa 'yan matan dake wannan harka,

Cikin tattaunawar da aka yi da shi Alhaji Tanimu Akawu a wani gidan radio ya yi bayanin cewa kimanin shekaru 'dai 'dai har goma sha takwas kenan yana sana'ar Fim a Kannywood amma bai mallaki dokiyar da wadansu 'yan mata suka mallaka cikin shekaru kadan ba.

Cikin hirar da akayi da Dattijon a wani gidan radio mai suna Human Right dake Abuja cikin wani shirin su mai suna DANDALIN FINA FINAI
Alhaji Tanimu ya bayyana cewa 'yan matan na Kannywood kawai suna bin maza ne kama daga masu kudi zuwa 'yan siyasa,

Tanimu Akawu ya ci gaba da cewa Motar da wata 'yar wasa take hawa a yanzu zata iya siyen motoci guda 10 da yake da su"

Yaci gaba da cewa, 'Yan matan sun mayar da Fim madubi ne, duk macen da kaji tace za ta yi harkar fim, tana so a haskata ne karshe ta fake da bin maza domin ta samu kudi."

Jarumin ya bayar da misali da wata sabuwar jaruma, a inda ya ce, "Kallo kawai ta zo yi aka sanyata a cikin fim, amma yanzu wayoyin dake hannunta sun kai na kimanin dubu dari takwas, kasan kuwa ba a fim ta samu wannan kudin ba, saboda nawa ne duka ake biya a fim din?"

Ya cigaba da cewa, "Ko ni yanzu bazan auri 'yar Fim ba, saboda na san abinda ke tafiya a harkar, yarinya tun ba ta da wayo take kallon mu muna yin fim amma yanzu ta zo cikin shekara daya ta samu kudin da bamu taba tunanin zamu samu ba, yaya za ayi ta dinga ganin girman mu."

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.