Friday, July 5, 2019




An gurfanar da wani zakara a kotu

Home An gurfanar da wani zakara a kotu

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Wata kotu a kasar faransa ta fara zaman sauraron wata shari'a kan wani zakara da ake kira Maurice bayan da wadansu ma'aurata suka shigar da kara a kan sa,

Su dai ma'auratan biyu sun zargi zakaran ne da laifin takura musu da yake yi da carar sa mai tsananin karfi
Shi dai wannan zakara wanda carar da yake yi da asubahi ke harzuka makwabta ya jawo hankalin mutanen kasar tare da shigar da shi gaban kotu domin aiwatar da hukunci,

Sai dai a cewar ta ita mai zakaran Corinne Fesseau cewa tayi zakaranta yana yin abun da duk wani zakara ke yi ne ba wani sabon abu ba"

Sai dai a zaman sauraron karan da aka yi a garin Roche fort masu shigar da karan basu samu halarta ba,
Sai dai shi zakaran wanda fitacce ne sananne a wannan yanki ya samu goyon baya daga wadansu masu zakaru wadanda suka yi cincirindo a farfajiyar kotun,


Su dai masu shigar da karan Jean Louis da matar sa Joelle Andrieus sun gina kayataccen gidan su na shakatawa ne a wani kauye da ake kira Saint Pierra d Oleron tun kimanin shekaru (15) da suka gabata sai kuma daga baya suka dawo zama gidan bayan ritayar su daga aiki
Sun ce kwanciyar hankali ce dalilin su na yanke shawarar zama a wannan yanki to sai dai sun ce Maurice da carar sa sun hana su sakat a inda sukace ya fara wannan kara mai karfi ne a shekarar 2017"

"Kuma kafin mu shigar da wannan kara mun yi korafi ga mai zakaran a cewar su"
Lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakanin su,

A yanzu dai kotun ta sanya watan satumba a matsayin ranar da zata duba domin yanke hukuncin da ya dace.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.