Wadandu muhimman abubuwa da baku sani ba game da MTN PULSE TARIFF PLAN
Hakika zamu iya cewa tsarin MTN Pulse na kamfanin sadarwar MTN NIGERIA tsari ne da kusan ba wani Kamar sa da ya kunshi wadannan abubuwa da zamu ambato nan nan gaba,
Wannan tsari ya kunshi garabasa mai tarin yawa ta fannin kira da kuma tsarukan shiga yanar gizo gizo
Ga kadan daga cikin abubuwan da MTN pulse tariff plan ya kunsa
1' Zaka kira ko wane layi a kwabo 11 duk second
Kenan minti 1 ya kama #1.60 wato naira daya da kwabo sittin
2' Zaka iya siyen 1gb na shiga yanar gizo a Naira 500 kacal Wanda wanda idan a wani tsarin ne Naira 1000 zaka sayi 1gb din,
3' Zaka iya shiga yanar gizo daga 12:00am har zuwa 4:00am a kan kudi Naira 25 kacal
4 ' Zaka iya siyen 250Mb akan kudi Naira 100 kacal
Ko 1gb a Naira 200
Ko 4gb a Naira 1000
5' Zaka samu kyautar 10Mb a duk sati idan ka saka katin Naira 100
6' Zaka iya samun 100mb da mintuna 12 na kiran ko wane layi a Naira 100 kacal
7' Zaka iya Kira Free daga 12:00am har zuwa 4:00am idan kana da a kalla Naira 100 a cikin akawun din ka ba tare da sun caji ko sisi ba ciki,
Me ya rage?
Yadda ake hijira zuwa MTN pule danna *406*1# kai tsaye zaka samu shiga tsarin
Sai dai idan ka shiga wani tsari a baya kuma bai cika kwanaki 30 ba to zasu caje ka Naira 100 kudin Hijira,
Dan haka ka jira har layin ka ya cika kwanaki 30 tsakanin canza tsaruka.
Zamu dakata anan sai kuma lokaci na gaba
Kuci gaba da bibiyar ZaurenHausa
Zaku iya share ta Social media domin wadansu su amfana
0 Comments:
Note: Only a member of this blog may post a comment.