Saturday, June 29, 2019




Yadda zaka duba lambar wayar ka a layukan sadarwa na Nigeria

Home Yadda zaka duba lambar wayar ka a layukan sadarwa na Nigeria

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Barkan ku da kasancewa da mu a wannan lakaci.
A yau muna tafe da yadda zaka duba lambar wayar ka a layukan sadarwa na Nigeria.

Sau da yawa zaka samu mutum ya sayi sabon layi ko ma ya dade yana amfani da shi amma da zarar ka tambayeshi lambar sa sai ya fara kame kame kasancewar bai haddace ta ba sannan bai San yadda zai gano ta kai tsaye ba. To idan kuna biye da ni daga yau wannan matsala ta zo karshe

Ba tare da bata lokaci ba ga yadda zamu yi domin ganin lambobin ku a layukan sadarwa na Nigeria.

Farko zamu fara da MTN yadda zaka duba lambar ka a layin MTN shi ne danna *123*1*1# nan take lambar ka zata bayyana a fuskar wayar sannan zasu turo maka ta sako.

Sai kuma Airtel Ng
Yadda zaka duba lambar ka a layin Airtel shi ne ka danna *121* zasu baka zabi sai ka yi relay da 3 zasu kara baka zabi sai ka yi relay da 4 nan take lambar ka zata bayyana ko ka danna *121*3*4# kai tsaye.

Sai 9Mobile

Yadda zaka duba lambar ka a 9Mobile shi ne ka danna *248# nan take zasu turo maka lambar ka.

Sai Glo Ng
Yadda zaka duba lambar ka ta Glo shi ne ka kira wannan lambar
1244 nan take wata murya zata fada maka lambar ka.

Zamu dakata a nan

Kuci gaba da kasancewa da ZaurenHausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.