Sunday, September 15, 2019




Dalilin da yasa na daina fito wa a Fim Rashida Adamu

Home Dalilin da yasa na daina fito wa a Fim Rashida Adamu

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Rashida Adamu tana daya daga cikin Jarumai mata a Kannywood musamman a shekarun baya kafin daga bisani ta shiga harkokin siyasa a inda ta kai ga har Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bata mukami a gwamnatin sa,
A yanzu dai tana a matsayin mai bawa gwamnan na #Kano shawara kan harkokin mata hakan haifar da dakatar da ita daga sana'ar da aka santa da ita wato Hausa Fim,

Wace ce Rashida Adamu?

Anhaifi Rashida Admu a karamar hukamar Tarauni a jihar Kano ta yi karatun firamare a Taraunin a daga bisani ta wuce zuwa jihar Jigawa ta yi Sakandren mata a Garki daga nan ta wuce zuwa wata makaranta mai suna Ma'haj a kasar Sudan a inda ta yi karatun Diploma daga nan ta wuce wata makarantar Jami'a a birnin Kwatano dake kasar Benin ta yi digiri a bangaren kimiyyar siyasa daga baya ta dawo ta stunduma a harkar Fina-finan Hausa,

Fim din ta na farko shi ne Jariya sai kuma Fim din da ya fito da ita wato Sa'a wanda ita ce ta shirya shi da kudin ta
Taci gaba da firo wa a Finafinai kamar su Tutar so Gobe da nisa Halwa.,

A yanzu dai likafar Rashida ta ci gaba tun tana fito wa cikin fim din wadansu har ta kai tana yin nata na kanta a karkashin kamfanin ta har kuma yanzu ta zo ta shiga cikin harkar siyasa kuma Allah ya sanya mata  albarka aka bata mukamin Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Mata kuma kasancewar wannan aiki ne na zuwa Ofis hakan ya sanya ta dakatar da fito wa a Fim sabo da karancin lokaci.



Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.