A yau zamu yi magana ne game da Airtel Double Data shi dai wannan tsari kusan duk mai ta'ammali da yanar gizo da Layin Airtel ya san shi,
Yadda abun yake shi ne idan kana kan wannan tsari to duk lokacin da ka sayi damen shiga yanar gizo ta hanyar *141# to zasu ninka maka 2 ne,
Wato idan ka sayi 1gb zaka samu 1gb kyauta kai ko ma MB nawa ka saya kana da ninkin sa ne,
Yadda ake shiga wannan tsari ba abu ne mai wahala ba sai dai fa wani lokacin sukan ki amincewa idan layin yana cikin waya da ake shiga yanar gizo da ita
Sabo da haka duk wanda ya gwada a wayar sa ta shiga yanar gizo suka ki karbar bukatar sa to ya gwada cire layin ya samu karamar waya ta kira kamar Nokia ya saka layin a ciki ya jarraba da yardar Allah zai samu karbuwa,
Yadda ake shiga tsarin Airtel Double Data shi ne Tura GET ta sakon SMS zuwa 141.
Ku yi share a Social Media Domin Wadansu Su Amfana
0 Comments:
Note: Only a member of this blog may post a comment.